Za a ci gaba da tashe-tashen hankula muddin ba a warware koke-koke da bambance-bambance dake tsakanin Falasdinawa da Isra’ila ba.
Rikicin da ake ciki a yanzu ya taso ne sakamakon watsi da ka’idojin Majalisar Dinkin Duniya da kuma yadda bangarorin biyu suka kasa daina kai hari kan fararen hula.
- Matashin Dan Kwallon Barcelona Guiu Mai Shekaru 17 Ya Jefa Kwallon Farko A Kungiyar
- “Hanyar Siliki Ta Dijital” Na Ingiza Zamanantar Da Duniya
La’akari da wannan matsalar ne Shugaban kasar Sin Xi Jinping, a yayin ganawarsa da firaministan Masar Mostafa Madbouly a nan birnin Beijing a ranar 19 ga watan Oktoba, ya bayyana cewa, “Muhimmiyar hanyar warware rikicin Palasdinu da Isra’ila da ke ci gaba da tabarbarewa, ita ce aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma game da shirin kafa ‘kasashe biyu’, wato kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta, ta yadda za a tabbatar da zaman lafiya tsakanin Falasdinu da Isra’ila.”
Hanyar tabbatar da zaman lafiya ba hanya ce mai sauki ba, amma ana iya farawa da fahimtar bukatun dukkanin bangarorin dake cikin rikicin. Rikicin Isra’ila da Falasdinu ba shi ne tushen matsalar ba, sai dai ya samo asali ne daga wani yanki na babban yanayi na duniya wanda ke cike da zalunci da tsangwama, da halin mamaya da karfafa rarrabuwar kawuna. Wajibi ne a tunkari cibiyoyi da ra’ayoyin dake haifar da rarrabuwar kawuna da suka hada da na leken asiri bisa muradun kasashen yamma da wasu kafafen yada labarai masu rura wutar fitina, da kuma magance dukkan batutuwan da suke da nasaba da wanann rikicin da ba a san ranar karewarsa ba.
Ya zama dole bangarorin da ke rikicin su yi la’akari da kiran da kasashen duniya suka yi na samar da “kasashe biyu” masu cin gashin kansu. Dole a fitar da Falasdinawa daga ukubar Isra’ila, kana, a bar su su mallaki kasarsu bisa tsare-tsare da ka’idoji da al’adun Falasdinawa kuma daidai da bukatunsu da dabi’unsu.
“Warware matsalar ta hanyar samar da kasashe biyu” na iya karfafa ci gaban tattalin arziki, saboda zai ba da ingantaccen tsarin tantance kan iyakoki, da inganta kasuwanci da tsaro ga Isra’ila da Falasdinawa. Kowace kasa za ta iya sanya nata matakan kasuwanci da tsaro da suka dace da al’ummarta da bukatunta idan an fayyace iyakokinta da kyau. Neman ci gaban tattalin arziki da inganta rayuwar Falasdinawa dake zaune a cikin kasa mai cin gashin kanta zai samar da zaman lafiya da wadata a yankin.
Babban abin takaicin shi ne, matsayin birnin Kudus a halin da ake ciki, da hakkin ’yan gudun hijirar Falasdinawa da aka dade ana ketawa, da kuma wuraren da Isra’ila take matsugunai a yammacin gabar kogin Jordan, na daga cikin manyan kalubale da cikas ga aiwatar da shirin na samar da “kasashen biyu”. Don warware wadannan matsalolin da samun ci gaba ga yarjejeniyar zaman lafiya mai dorewa, dole ne a yi nasara ta hanyar diflomasiyya da sasantawa.
Taimakon da kasar Sin take baiwa kokarin kasar Masar na kafa hanyoyin jin kai da kuma aniyyarta na inganta hadin gwiwa da kasar Masar da sauran kasashen Larabawa, wani mataki ne kan hanyar da ta dace ga jin kan Falasdinawa. Shugaba Xi ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta hada karfi da karfe tare da Masar da sauran kasashen Larabawa don inganta hadin gwiwar tattalin arziki a fannoni daban daban.
Zubar da jinin dake gudana ya zama gargadi mai ban tsoro na abin dake faruwa sa’ad da kuskure, da rarrabuwa kawuna, da rashin yarda suka ci gaba da wanzuwa. Abin takaici, bangarorin da abin ya shafa sun kasa ba da fifiko ga kariyar fararen hula, da rungumar akidar tabbatar daidaito da fahimta, da kuma sanin yadda gwagwarmayarsu ke da alaka da juna domin koyo daga kura-kurai. Ba abin mamaki ba ne suka kasa cimma manufar dawwamar da zaman lafiya ta hanyar ajiye bambance-bambancen da ke tsakaninsu.
Yin aiki tare, tsakanin Sin da kasashen Larabawa, musamman Masar, na iya ba da gudummawa ga irin wannan kuduri na lumana tsakanin Isra’ila da Falasdinu. Karfafa tsagaita bude wuta, kaddamar da kasuwanci da fadada tattalin arziki, da hadin gwiwar diflomasiyya, duk suna aiki tare don samar da yanayin da zai dace da tattaunawar zaman lafiya da kuma matakan da aka amince da su.