Yayin da tsarin gina shawarar ziri daya da hanya daya ke shiga sabon mataki na ci gaba mai inganci, ci gaban tattalin arzikin duniya na dijital shi ma na kara ingiza sabbin damammaki.
Yayin taron BRF karo na 3 da aka kammala, Sin ta gabatar da shawarar kirkirar yankin gwajin hadin gwiwar gudanar da cinikayyar dijital na hanyar siliki, tare da gudanar da “Baje kolin kasa da kasa na cinikayyar dijital” a kowace shekara.
- Taron BRF Ya Cimma Daruruwan Nasarori
- Rikicin Gaza: Ana Ci Gaba Da Tir Da Kisan Fararen Hula A Harin Asibiti
Kaza lika, Sin da kasashe masu alaka da batun, sun yi hadin gwiwar fitar da tsarin aiki na Beijing, domin hadin gwiwar kasa da kasa a fannin raya tattalin arziki na dijital, na ziri daya da hanya daya, da sauran takardun bayanai masu kunshe da sakamakon da aka cimma yayin taron. Sassan kasa da kasa da dama sun amince cewa, wannan mataki zai ingiza zurfafawa, da dunkulewar hadin gwiwa a fannin raya tattalin arziki na dijital tsakanin Sin da kasashe abokan tafiya a harkar.
A halin da ake ciki, al’ummun duniya na fuskantar mataki na 4, na juyin juya halin masana’antu mai kunshe da amfani da fasahohin sadarwa, da hade sassa daban daban, da tattara bayanai masu nasaba. A daya bangaren kuma, sakamakon gibin fasahohin dijital, kasashe masu tasowa ba sa cin cikakkiyar gajiya, da nasarori daga sauye sauye da fasahohin digital ke haifarwa, wanda hakan ke yi musu tarnaki, wajen cimma nasarar zamanantarwa.
Shekaru 10 da suka gabata, Sin ta kaddamar da shawarar gina ziri daya da hanya daya. Kuma bisa kwazon kasar na shiga ayyuka masu nasaba, da yayata manufar, an kai ga cimma manyan nasarori karkashin tsarin “Hanyar siliki ta dijital”. (Mai fassara: Saminu Alhassan)