A yau Talata, kasar Sin ta yi nasarar harba sabon tauraron dan Adam da ake iya sarrafawa daga nesa zuwa sararin samaniya, daga cibiyar harba taurarin dan adam ta Xichang dake lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar.
Rokar Long March-2D ne ya harba tauraron na Yaogan-39 da misalin karfe 4:03 na sanyin safiyar yau, agogon Beijing.
Wannan shi ne karo na 492 da aka yi amfani da dangin rokar Long March wajen harba tauraron dan Adam. (Fa’iza Mustapha)