Kasar Sin ta harba wani sabon tauraron dan Adam da ake sarrafawa daga nesa, daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar, jiya Lahadi da misalin karfe 11:44 na rana agogon Beijing.
Linzamin Long March-4C ne ya harba tauraron mai suna Yaogan-33 zuwa sararin samaniya. Wannan shi ne karo na 357 da aka harba tauraro bisa amfani da linzamin Long March. Linzami ya kuma harba wani karamin tauraro mai binciken fasaha.
Za a yi amfani da taurarin biyu domin binciken kimiyya da safiyon albarkatun kasa da kiyasta amfanin gona da karewa da rage aukuwar annoba. (Fa’iza Mustapha)