A yau Alhamis 26 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta jaddada cewa, matsayin da kasarta ta dauka ya dogara ne kan gaskiya da adalci, kuma yana mai da martani da kakkausar murya ta kasa da kasa, musamman ma ta kasashen Larabawa.
Jami’ar ta bayyana haka ne a yayin da take amsa tambayar da aka yi kan kin amincewar da kasar Sin ta yi game da daftarin kudurin halin da Falasdinu da Isra’ila ke ciki a kwamitin sulhu na MDD.
- Xi Jinping Ya Gana Da Gwamnan Jihar California Dake Amurka
- UNESCO Ta Yi Bikin Ranar Amfani Da Kafofin Watsa Labarai Da Yada Bayanai Ta Duniya A Abuja
Jami’ar ta nuna cewa, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya riga ya yi karin haske kan matsayin kasar Sin a dukkan fannoni a jawabin da ya gabatar bayan kada kuri’a a kwamitin sulhu na MDD. Jami’ar ta kuma jaddada cewa, kasar Sin ba ta da wani muradi na son kai kan batun Falasdinu. Kasar Sin tana goyon bayan duk abin da zai taimaka wajen samar da zaman lafiya, kuma za ta yi iyakacin kokarinta wajen yin sulhu tsakanin Falasdinu da Isra’ila.
A ranar 25 ga watan Oktoba, kasashen Rasha da Sin sun yi watsi da daftarin kudurin kwamitin sulhu na MDD kan halin da ake ciki tsakanin Falasdinu da Isra’ila da Amurka ta tsara, sannan Hadaddiyar Daular Larabawa ita ma ta kada kuri’ar kin amincewa da shi. Baya ga haka, sakamakon adawar da kasashen Amurka da Birtaniya da wasu kasashe suka yi, ba a amince da daftarin kudirin da Rasha ta tsara ba.
Bugu da kari, kakakin hukumar kula da hadin gwiwar ci gaban kasa da kasa ta kasar Sin Xu Wei ya bayyana a yau Alhamis cewa, gwamnatin kasar Sin za ta sake ba da wani rukunin agajin gaggawa na Yuan miliyan 15 kwatankwacin dalar Amurka Miliyan 2.05, da suka hada da abinci da magunguna ga Gaza.
Xu ya kara da ce, kasar Sin tana bakin cikin ganin yadda rikicin Falasdinu da Isra’ila ya haifar da hasarar rayukan fararen hula da dama da kuma tabarbarewar yanayin jin kai a Gaza.
Ya kara da cewa, don taimakawa wajen shawo kan matsalar jin kai a Gaza, kasar Sin ta riga ta ba da tsabar kudi dalar Amurka miliyan 1 ta hannun hukumar ba da agaji ta MDD mai kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinu a gabas ta kusa da kuma hukumar Falasdinawa a lokuta daban-daban.
(Mai fassara: Bilkisu Xin)