Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yaba wa kotun koli akan hukuncin da ta yanke na tabbatar da shugaban kasa Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023.
Buhari a cikin sanarwar da mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Alhamis, ya yi kira ga ‘yan jami’yyun adawa da su hada hannu don yin aiki da gwamnatin Tinubu.
Tsohon shugaban ya fitar da sanarwar ‘yan mintuna kadan bayan kotun ta yi fatali da daukaka karar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP Peter Obi da takwaransa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, suka shigar a gaban kotun.
Kazalika sanarawar ta ce, “Ganin cewa a yanzu mun kai madakata bayan shafe watanni takwas ana fafatawa a shari’ar, a yanzu komai ya zo karshe, inda ya yi nuni da cewa, ‘yan adawar sun yi fafatarwa da ta dace a gaban kotun.”
Bugu da kari, ganin cewa ‘yan jami’iyyun adawar sun bi kadinsu a gaban kotun yadda ya kamata kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba su dama, ya kamata su mika hannun ci gaba da abota ga Tinubu da Shettima da kuma gwamnatin APC.
A cewar sanarwar, “Ya kamata ‘yan jam’iyyun adawar su sakar wa gwamnati mai ci mara don ta ci gaba da gudanar da shugabanci don ‘yan Nijeriya su amfana da gwamnatin APC.”