ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

A Tausaya Wa Talaka

by Leadership Hausa
3 years ago
Talaka

A watan Agusta na wannan shekarar mun yi sharhi mai taken ‘Bukatar A Tausaya Wa Talakawa”, mun sake dawo da sharhin ne saboda muhimmancinsa, musamman ganin rahotannin da ke fitowa na shirin karin kudin makaranta da gwamnati ke yi a fadin kasar nan. Damuwarmu a nan ita ce, in har wannan labari ya zama gaskiya zai kara matsalar da al’umma ke ciki ta matsin tattalin arziki a daidai wannan lokacin da al’amuran rayuwa ke kara ta’azara a kullum.

Muna kira ga gwamnati ta rika sa talaka a zuciya a yayin shiri da kuma gabatar da dukkan al’murranta.

  • Da Ɗumi-ɗuminsa: Kotun Ƙoli Ta Yi Fatali Da Ƙarar Atiku Da Obi, Ta Tabbatar Da Nasarar Tinubu
  • Sabon Tsarin Biyan Albashi: Gwamnati Za Ta Cire Ma’aikatan Da Ba A Tantance Su Ba, Gobe

A duk fadin duniya ana samar da gwamnati ce musamman domin ta kula da jin dadin al’umma da kuma tabbatar kare rayuka da dukiyoyinsu. A kan haka dole kowacce gwamnati ta nuna damuwarta a kan jin dadin al’ummarta.

ADVERTISEMENT

Tausaya wa talakawa a cikin harkokin gwamnati abu ne da ya kamata a fuskanta a matsayin hakki. Kowanne dan kasa na bukatar ya samu damar gabatar da abin da ya shafe shi daidai da kowa da kuma damar samun nasara a kan abin da ya sa a gaba, ba tare da nuna bambancin tsakanin talaka da mai kudi ba. Idan har an samar da tsare-tsare da suka ba talakawa muhimmanci, gwamnati na nuna cewa, ta tsayu ne don tabbatar da adalci ga dukkan bangarorin al’umma kamar yadda yake a cikin kundin tsarin mulkin kasa, sannan hakan na nuna cewa, lallai gwamnati ta dauki rayuwa da mutuncin al’umma da matukar muhimmanci.

Bayanai na nuna cewa, samar da jin dadin al’umma shi ne, gwamnati ta sanya ido tare da tabbatar da jin dadin al’ummarta ta hanyar ba dukkan bangarori hakokinsu ba tare da nuna bambanci ba, tare da raba dukiyar gwamnati ga dukkan bangarori na al’ummar kasa don su ma su san ana yi da su.

LABARAI MASU NASABA

Arsenal Na Dab Da Ɗaukar Jeremy Monga Daga Leicester City

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

A kasa kamar Nijeriya da ke da bambance-bambance a tsakanin talaka da mai kudi da sauransu, ya zama dole gwamnati ta muhimmantar da abubuwan da suka shafi jin dadin al’umma musamman na mutane da ake nuna wa wariya da bambanci a cikin al’umma. A matsayinmu na gidan jarida, wannan ne hanyar da muke bukatar shugabannin gwamnnati su dauka domin cimma manufar ingantar rayuwar al’umma.

A ra’ayinmu, al’umma na samun ci gaban da ya kamata ne ta hanyar daga masu rauni a cikinta. A kan haka ya zama dole gwamnati a dukkan matakai su samar da manufofin da za su karfafa talakawa ta yadda su ma za su nunfasa, su kuma shiga cikin tsare-tsaren da gwamnati ke fito da su na ci gaban al’umma gaba daya. Duk da muna sane cewa, wasu kudurorin gwamnati na daukar lokaci kafin su iya tsayuwa da kafafunsu amma kuma yana da muhimmanmci a samar da gwamnatin da za ta tafi tare da talakawa a kuma ba su damar bayar da tasu gudummawar ga bunkasar tattalin arzikin kasa.

A bayyana yake cewa, al’ummar Nijeriya da dama na fuskantar matsanancin talauci, miliyoyin ‘yan Nijeriya ke fafutukar ganin sun samu abin kaiwa bakin salati. Idan gwamnati ta muhimmantar da al’amarin talaka a cikin tsare-tsarenta to lallai tamkar ta yi nasarar yaki da talauci ne daga tushe, kamar abin da ya shafi rashin aikin yi, rashin samun ilimi mai inganci da cikakken kiwon lafiya da kuma abubuwan da suka shafi jin dadin al’umma gaba daya. Samar wa talakawa tsare-tsaren gwamnati masu muhimmanci zai taimaka wajen kubutar da su daga kangin talauci tare da samar da daidato a cikin al’umma.

A matsayinmu na gidan jarida mun damu kwarai da gaske a kan yadda ake samun tashin-tashina sakamakon rashin adalci da daidato a cikin al’umma. Watsi da bukatun talakwa da kuma rashin sanya su a cikin tsare-tsaren ci gaba na iya takura su, ya sa su cikin damuwa, wanda hakan zai iya zama tushen tayar da hankulan al’umma. Samar wa talakawa hanyoyin sararawa tare da sanya su a cikin tsare-tsaren bunkasar tattalin arzikin kasa, zai sa talakawan su rage kuncin rayuwa, ya sa su rungumi sauran al’umma, kana su kudiri aniyar kare ci gaban da ake samu a cikin al’umma don sun san su ma suna da nasu kason a ciki. Amma abin takaici a nan shi ne, wannan ba shi a cikin tunanin gwamnatin da muke da shi a dukkan matakai a wannan lokacin.

Yana kuma da matukar muhinmmanci a fahimci cewa, duk wani dan’adam yana da baiwar da Allah ya yi masa ba tare da bambancin talaka da mai kudi ba. Idan har gwamnati ta samar wa talakawa ingantaccen ilimi, aikin hannu da kiwon lafiya a cikin sauki, tamkar ta bude wasu kofofi ne da za a samar da al’ummar da za ta bayar da gudummawar bunkasar tattalin arzikin kasa. Zuba jari wajen bunkasa rayuwar talakawa ba wai yana amfanar da mutanen da suka samu tallafin kadai ba ne amma hakan yana tabbatar da ci gaba mai dorewa a bangaren tattalin arazikin kasa gaba daya.

Muna amfani da wannan damar wajen tunatar da gwamnati cewa, ci gaban kasa ba zai samu nasara ba idan har aka yi watsi da bukatun talaka. In har gwamnati ta samar da tsare-tsaren bai-daya da zai karfafa talakawa, to gwamnati ta hau hanyar samar da kakkarfar al’umma da soyayya wadda amince wa juna zai yi tasiri a tsakaninsu.

Yayin da gwamnati ke samar da sauye-sauye a bangarorin mulki da dama a cikin wata biyu da suka wuce, yanzu ya zama dole ta tabbatar da dukkan bangarorin al’umma sun shiga cikin shirin ba tare da nuna bambanci ba.

A kan haka muke ba gwamnati shawarar cewa, ta samar da tsare-tsaren da za su rage radadin talauci a cikn al’umma, musammnan ganin yadda aka cire tallafin man fetur, ya kuma kamata a gudanar da wannan cikin sauri ba tare da boye-boye ba.

Talaka
Leadership Hausa
+ postsBio
  • Leadership Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/leadership-hausa/
    Jerin Gwarazan Taurarinmu
  • Leadership Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/leadership-hausa/
    Jerin Gwarazan Taurarinmu
  • Leadership Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/leadership-hausa/
    “Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”
  • Leadership Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/leadership-hausa/
    Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati Na Shekarar 2025, Dakta Zacch Adedeji

MASU ALAKA

Arsenal Na Dab Da Ɗaukar Jeremy Monga Daga Leicester City
Wasanni

Arsenal Na Dab Da Ɗaukar Jeremy Monga Daga Leicester City

June 4, 2026
Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili
Manyan Labarai

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro
Manyan Labarai

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Next Post
Bashin Naira Biliyan 2.5: Duhu Ya Mamaye Ma’aikatun Sakkwato Da Zamfara

FALLASA: HUJJOJI KAN YADDA BELLO MATAWALLE YA KWASHE BILIYOYI DA SUNAN AIKIN TASHAR JIRGIN SAMA A ZAMFARA

LABARAI MASU NASABA

Sin: Ya Kamata Tarayyar Turai Ta Dubi Huldar Tattalin Arziki Da Ciniki Tsakaninta Da Sin Bisa Daidaito

Sin: Ya Kamata Tarayyar Turai Ta Dubi Huldar Tattalin Arziki Da Ciniki Tsakaninta Da Sin Bisa Daidaito

June 4, 2026
Arsenal Na Dab Da Ɗaukar Jeremy Monga Daga Leicester City

Arsenal Na Dab Da Ɗaukar Jeremy Monga Daga Leicester City

June 4, 2026
An Gudanar Da Taron “Tattaunawar Magadan Garuruwa Na Duniya Na 2026” A Birnin Beijing

An Gudanar Da Taron “Tattaunawar Magadan Garuruwa Na Duniya Na 2026” A Birnin Beijing

June 4, 2026
Atiku Ne Ya Fi Dacewa Da Tikitin Takara A ADC Amma Ya Kamata Ya Janye — Baba-Ahmed

2027: Kasancewa Ɗan Arewa Kaɗai Ba Zai Tabbatar Da Samun Ƙuri’u Ba – Baba-Ahmed

June 4, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

June 4, 2026
Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

June 4, 2026
Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.