Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Adon Da Kwalliya. Yau za mu yi magana kan kan gyaran jiki ciki da waje. Ga yadda yake kamar haka:
Uwargida yadda ake gyaran jiki idan kina so gyaran ya yi kyau kar ya bar miki wani tabo-tabon baki har ma a fuska, ki kasance kina gyaran jikinki da safe ko kuma da yamma, ba’a gyaran jiki da rana, idan kika kasance mai gyaran jiki da rana za ki ga wani tabo ya yana fito miki sai ki ga can ya yi baki can ya yi haske jikinki zai yi dabbare- dabbare amma idan da safe kike yi ko da yamma rana ta yi sanyi in sha Allah jikinki zai yi kyau kuma ba zai yi wannan dabbare-dabbaren ba.
Abubuwa da Uwargida za ki tanada
Za ki samu kankana ki yi bilandin dinta, sannan ki samu zuma ko yagot duk wanda kika samu za ki iya amfani da shi sai ki zuba zuman ko yagot din a cikin kankanarki gauraya sai ki je ki shafe jikinki da shi ki barshi ya yi kamar minti talatin zuwa awa daya sai ki murje jikin ki sannan ki yi wanka za ki ga abin mamaki.
Amfanin bakin ridi:
Uwargida za ki samu bakin ridi ba fari ba, baki a kwaishi yana nan.
Yana gyara jikin mace sosai yana da amfani, ko auren ‘ya za a yi za a iya yi mata amfani da shi wajen gyara amarya.
Za ki samu bakin ridi ki soya shi, ki nika shi tare da su citta da kanunfari, sannan ki samu naman ki idan kika dafa namanki, ki kwaba shi da hadin bakin ridin ki ci ko kuma ki rika dangwala kamar yaji kina ci. Yana da amfani sosai yana gyara mace, koda a wata-wata ne kamar bayan kin gama al’ada Uwargida ki daure ki rika yi.
Sannan ko farin ridin shima yana da amfani sosai wajen dahuwar kaza, idan kika samu yajin dahuwar kaza ki samu farin ridinki, ki daka shi idan kika zo dahuwar kazar bayan kin zuba yajin dahuwar sai ki zuba wannan farin ridin da kika daka a cikin dahuwar kaza yana da kyau sosai.