Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya ziyarci gidan gyaran halin da ke Kuje a babban birnin tarayya Abuja, inda ‘yan ta’adda suka kai hari tare da shafe sama da minti 30 suna cin karensu babu babbaka.
Bayan da ya saurari bayanan da aka masa tare da duba wuraren da ‘yan ta’addan suka barnata, shugaba Buhari ya gana da ‘yan jarida, inda ya nuna takaicinsa da tsarin tattara bayanan sirri na Nijeriya da yadda ake tafiyar da tsarin.
- Da Dumi-Dumi: Mune Muka Kai Hari Gidan Yarin Kuje – ISWAP
- Kotu Ta Yanke Wa Wani Matashi Dan Kasar Nijar Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Laifin Kisan Kai A Kebbi
“Gaskiya ban ji dadi da tsarin tattara bayanan sirri ba. Ta yaya ne ma har ‘yan ta’adda za su iya kimtsawa da shirya makamai, su kai hari cibiyar tsaro kuma su yi tafiyarsu?”
Buhari wanda ya samu rakiyar sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya ce, bayan ziyarar yana bukatar a ba shi cikakken rahoton yadda harin ya gudana.
Buhari ya yi amfani da wannan damar wajen maida martani kan sukar da wasu ke ta yi kan ziyararsa zuwa birnin Dakar na kasar Senegal a daidai lokacin da ake jimamin harin, ya ce gwamnati ba za ta tsaya da aiki don kasa na fuskantar barazanar tsaro ba.
“In aka soke yin tafiyar ‘yan ta’addan sun yi nasara kenan da sunan harbe-harbe, wanda kuma babu wata gwamnatin da zata amince da hakan a duk duniya,” a cewarsa.