Mayakan Boko Haram da ke ayyukansu a yammacin Afirka ta dauki nauyin kai hari gidan yarin Kuje da ke babban birnin tarayya Abuja, a daren ranar Talata.
Rahotanni sun bayyana yadda fursunoni sama da 800 suka tsere bayan fasa gidan yarin da kashe wasu daga cikin jami’an tsaron da ke gadin gidan yarin.
- Atiku Ya Nesanta Kansa Daga Rikicin Cikin Gida Na PDP A Ekiti
- Buhari Ya Tafi Senegal Don Halartar Taron Kasa Da Kasa Na Kungiyar Hadin Kan Kasashen Afirka
Da farko an yi zargin ‘yan bindiga ne suka kai harin gidan yarin, baya ga wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai kan ayarin tawagar shugaban kasa a Jihar Katsina.
Amma hukumar da ke kula da gidajen yari ta Nijeriya, ta musanta rade-radin da ake na cewar jami’im dan sanda, DCP Abba Kyari tare da wasu sun tsere bayan harin gidan yarin.
A ranar Laraba ne shugaba Buhari ya ziyarci gidan yarin, inda ya duba irin barnar da aka yi, wanda ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda al’amuran tsaron gidan yarin suke wakana.
Sai dai bayan ziyarar, Buhari ya tafi kasar Senegal inda zai halarci taron kasa da kasa na bunkasa kasashen Afrika.