Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta Ƙasa (INEC) ta wallafa cikakken bayanai kan katittikan masu zaɓe (PVC) da aka karɓa da waɗanda ba a karɓa a shirye-shiryen gudanar da zaɓuɓɓukan gwamna da za a yi a jihohin Bayelsa, Imo da Kogi a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamban 2023.
Hakan ya biyo bayan taron da hukumar ta yi a ranar Litinin domin sake nazarin shirye-shiryen da ta ke yi na zaɓuɓɓukan gwamna da za a yi a jihohin uku.
- Rikicin Gaza Ya Haifar Da Rashin Tabbas a Kasuwar Mai ta Duniya
- An Gudanar Da Taron Tattaunawa Kan Raya Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Tsakanin Sin Da Girka
A sanarwar da Babban Kwamishina kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai Da Ilmantar Da Masu Zaɓe na INEC, Mista Sam Olumekun, ya rattabawa hannu, hukumar ta ce: “Kamar yadda aka yi a zaɓuɓɓukan baya-bayan nan, ciki har da Babban Zaben Mayun 2023, hukumar ta wallafa cikakken bayani kan katittikan masu zaɓe (PVC) da aka karɓa da waɗanda ba a karɓa ba a jihohin uku a matakin rumfunan zaɓe.
“Haka kuma bayanin ya bada yadda aka rarraba rumfunan zaɓen a Yankunan Ƙananan Hukumomi, Mazaɓu, da sunayen rumfunan zaɓen, da alƙaluman lambobinsu, da yawan masu zaɓe da su ka yi rajista, da kuma yawan katittikan masu zaɓe da aka karɓa da waɗanda ba a karɓa ba.
“Lissafin na jihohin uku ya nuna cewa daga cikin masu zaɓe 1,056,862 da su ka yi rajista a Jihar Bayelsa, mutum 1,017,613 sun karɓi katittikansu, 39, 249 ba a karba ba. A Jihar Imo, masu zaɓe da su ka yi rajista sun kai 2,419,922, mutum 2,318,919 sun karɓi katittikansu, sai 101,0003 da ba su karɓa ba, yayin da a Jihar Kogi, daga cikin masu zaɓe 1,932,654 da su ka yi rajista, mutum 1,833,160 sun karɓi katittikansu, sannan 99,494 ba su karɓa ba.”
Hukumar ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a lamarin zaɓuɓɓukan da su yi la’akari da cewa, duk fa wata ƙuri’a da aka samu a rumfar zaɓe wadda ta haura yawan ƙuri’un da aka karɓa to shaida ce cewar an yi aringizo kuri’u.