Jam’iyyar APC ta shawarci tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar 25 ga watan Fabrairu, da ya yi hakuri ya amince da kayen da ya sha a matsayinsa na dattijon kasa.
Mista Felix Morka, sakataren yada labarai na jam’iyyar APC na kasa ne ya bayar da shawarar a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Abuja yayin da yake mayar da martani ga wani taron manema labarai da Atiku ya yi jawabi a safiyar ranar.
- Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Natasha Na PDP A Matsayin Sanatan Kogi Ta Tsakiya
- Karairayewar Darajar Naira: CBN Ya Ce Ba Shi Da Laifi, Ya Nemi A Kori Ƙarar Falana A Kotu
Morka ya ce: “Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP wanda ya yi jawabi a taron manema labarai a safiyar yau (Litinin), Har yanzu yana takaicin rashin nasararsa.
“Ya gabatar da dogon jawabi mai dauke da zarge-zarge, wanda bai dace ba kuma bai dace da tsohon mataimakin shugaban kasa ba.
“Atiku ya amayar da da’awar da ya yi na cewa, Shugaba Bola Tinubu bai ci zaben shugaban kasa a ranar 25 ga Fabrairu, 2023 ba a taron manema labarai.”
Duk zarge-zargen da Atiku ya yi na nunin cewa “zaben yana cike da kura-kurai, kotun daukaka kara da kotun koli sun yi watsi da karar ba tare da wata hujja kwakkwara ba.”
Kakakin na APC ya ci gaba da cewa, babu inda a cikin jawabin Atiku ya bayyana cewa ya lashe zaben.
Wannan, ya tabbatar da sakamakon da kotun ta yanke cewa, Atikun bai ci zabe ba.