Wasu mahara dauke da makamai sun kashe basaraken garin Garin Moddibo da ke jihar Taraba, Alhaji Muhammadu.
An sace matar sarkin, dansa da wasu mutane hudu a garin, wanda ke da tazarar kilomita kadan daga hedikwatar Sunkani da ke karamar hukumar Ardo- Kola a jihar, da misalin karfe 11:30 na daren ranar Litinin.
- Hukuncin Kotun Ƙoli: APC Ta Nemi Atiku Ya Yi Haƙuri Ya Rungumi Ƙaddara
- Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Natasha Na PDP A Matsayin Sanatan Kogi Ta Tsakiya
An kai wa wasu kauyuka biyu da ke makota da garin hari sannan an yi garkuwa da mutanen kauyen hudu ciki har da wata mai shayarwa.
Mafarauta karkashin jagorancin shugaban kungiyar mafarauta na jihar, Dantala Adamu, an ruwaito sun kai dauki dajin da tsaunuka a wani yunkuri na ceto mutanen da aka sace.
Shugaban karamar hukumar Ardo-Kola, Dalhatu Kawu, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma kara da cewa ya kai rahoton faruwar lamarin ga gwamnatin jihar Taraba.
“Karamar hukumarmu tana hannun ‘yan fashi suna garkuwa da mutanenmu ba dare ba rana kuma a yanzu haka rundunar ‘yansanda ta musamman da mafarauta suna bakin kokarinsu wajen ganin sun kai dauki.
Kakakin rundunar ’yansandan Jihar Taraba, SP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai yi karin haske kan lamarin ba.