Wasu jiga-jigan jamiyyar APC mai mulki da suka kasance daga cikin Deliget a zaben fidda-gwanin APC, Zakari Maigari da Zubainatu Mohammed,da, sun garzaya kotun tarayyar da ke Abuja, inda suka bukaci kotun da ta dakatar da APC daga sauya Kabiru Masari a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu.
Sun kuma bukaci kotun ta dakatar da hukumar zabe ta kasa (INEC), daga bukatar APC na sauya sunan Masari matsayin abokin takara na wucin gadi.
- Buhari Ya Fusata Game Da Harin Gidan Yarin Kuje, Yana Bukatar Amsa
- Jiragen Yaki Sun Kashe ‘Yan Bindiga 42 A Katsina
A cikin bukatar ta Zakari Maigari da Zubainatu Mohammeda da suka gabatar wa kotun, sun ce akwai bukatar amfani da sunan wanda aka bayar.
Tinubu dai bayan ya zamo zakara a zaben fidda-gwanin, ya mika wa INEC sunan Masari a matsayin wanda zai yi masa mataimaki amma a matsayin na wucin Gadi.
A cikin takardar korafin da suka gabatar wa kotun mai dauke da lamba FHC/ABJ CS/1059/2022 da ranar 4 ga watan Yunin 2022, sun bukaci kotun da ta fayyace musu, idan aka yi duba da sashe na 142 (1) da sashe na 29 (1) da sashe na 31 da kuma sashe na 33 na dokar zabe da aka sabunta wanda ke nuni da cewar jam’iyya ko dan takara ba su da hurumin sauya abokin takara.
Sun kama bukaci kotun ta fayyace musu cewa, idan aka yi duba da sashe na 142 (1) na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 da aka sabunta wanda ya bayar da damar tikitin hada na takarar shugaban da mataimakins, ko ya bayar da damar sauya sunan Masari a matsayin mataimakin Bola.
Sun kuma bukaci kotun ta sake fayyace musu, inda aka yi duba da sashe na 29 (1) da sashe 31 da kuma sashe na 33 na dokar zabe da aka sabunta ta 2022 ko za a iya sauya sunan Masari ba tare da an yi wani sabon zaben fidda-gwani ba don a sake fitar da sunan wani sabon dan tankarar shugaban kasa na APC.