Hadimin fitaccen Malamin addinin musulunci da ke Jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, Malam Tukur Mamu, ya ce wadanda suka kai hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ne suka kai hari kan gidan yarin Kuje da ke Abuja ne.
Kungiyar ‘yan ta’adda ta Ansaru da ta kai hari tare da yin garkuwa da fasinjoji a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris, ta dauki alhakin kai hari gidan yarin Kuje da ke birnin tarayya Abuja, a daren ranar Talata.
- An Bukaci Kotu Ta Dakatar Da APC Daga Sauya Masari A Matsayin Abokin Takarar Tinubu
- Harin Kuje: Buhari Ya Nuna Rashin Jin Dadinsa Kan Tsaron Kasar Nan
Malam Tukur Mamu, wanda babban mai shiga tsakani don ganin an sako fasinjojin da aka yi garkuwa da su a cikin jirgin kasa Abuja zuwa Kaduna.
Mamu ya ce kafin kai harin, ya shaida wa jami’an sirri tare da hukumomi yiwuwar kai hari amma sun kasa daukar mataki.
LEADERSHIP ta ruwaito yadda ‘yan ta’addan suka saki Manajan-Daraktan Bankin Manoma da wata mai ciki, daga bisani kuma suka sake sakin wasu mutane 11 da suka sace a cikin jirgin.
Tun daga wancan lokacin ‘yan ta’addan sun sha gargadin gwamnatin tarayya kan kin biyan bukatarsu tare da saurarensu, wanda ya sa suka fara barazanar kashe ragowar fasinjojin da ke hannunsu.
Da yake martani kan harin gidan yarin na Kuje, Mamu wanda hadimin Sheikh Gumi a kafafen watsa labarai, ya ce yana dab da daina shiga tsakani don sansanci tsakanin ‘yan ta’addan da gwamnatin tarayya, sakamakon halin ko in kula da gwamnatin ke nunawa a cewarsa.
Mamu ya ce rayuwarsa tana cikin hatsari, kuma idan wani abu ya same shi kada a zargi ‘yan ta’addan face tsarin shugabancin kasar nan.
Idan ba a manta ba Sheikh Ahmad Gumi ya yi gwagwarmaya a baya, don ganin ‘yan bindiga da suka addabi jihohin Kaduna, Neja, Zamfara da Sakkwato sun ajiye makamai tare da saduda.
Sai dai wasu daga tsagin gwamnati musamman ta jihar Kaduna, sun zargi shehun malamin da goya wa ‘yan bindigar baya wajen kai hare-hare.
Harin gidan yarin Kuje, ya bar baya da kura, inda dubban ‘yan Nijeriya ke tofa albarkacin bakinsu game da harin tare da kiran gwamnati ta kawo karshen tasirin ‘yan ta’adda.