Hukumar ‘yansanda ta tabbatar da Kayode Egbetokun a matsayin cikakken Sufeto-Janar na ‘yansanda na kasar nan.Â
Ministan kula da harkokin ‘yansanda, Ibrahim Geidam ne, ya sanar da hakan a ranar Talata a lokacin da ya gana da manema labarun fadar shugaban kasa da ke Abuja.
- Kotu Ta Yanke Wa ‘Yan Daudu 8 Hukuncin Daurin Watanni 3 A Kano
- Kwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Ethiopia Da Ci 4 A Abuja
Kazalika, Geidam wanda ya sanar da hakan jim kadan bayan kammala taron majalisar kasar wadda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta ya ce, majalisar ta amince da bukatar da Tinubu ya gabatar na amincewa da nadin Kayode a matsayin Sufeton ‘yansandan.
A cewarsa, Kayode ya kasance a matsayin mukaddashi tun bayan da aka nada shi watanni hudu da suka wuce, inda ya kara da cewa, bayanan da ke cikin takardun karatunsa suna da kyau kuma ya halarci kwasa-kwasai da dama.
Bugu da kari, ya bayyana cewa, Kayode ya ksanace mutum mai gaskiya kuma jajirtacce wanda hakan ya sa aka amince da bukarar Tinubu na tabbatar da shi a matsayin Sufeto ‘yansanda.
Shi ma a nasa jawabin gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule, ya bayyana cewa, jawabin da Kayode ya gabatar a lokacin zaman majalisar, ya nuna a zahiri Kayode ya san irin kalubalen rashin tsaro da Nijeriya ke fuskanta.
Shi kuwa gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun ya sanar da cewa, majalisar ta kuma tattauna akan bai wa rundunar ‘yansanda kudade don gudanar da ayyukansu.
Kazalika, gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya sanar da cewa, Tinubu ya kafa kwamiti na mussaman da zai samar da sauye-sauye don a saita rundunar ‘yansanda ta kasa yadda ta dace.