Babban Bankin Kasa (CBN), ya rufe bankuna guda 754 da suka hada da manya da matsakaita da kuma bankunan sayen gidaje a fadin kasar, sakamakon matsalolin da bankunan suka shiga.
Sai dai kuma hukumar kula da bankuna da sanya ido da kuma bada kariya ta hanyar Inshora da ake kira Nigeria Deposit Insurance Corporation NDIC, ta ce ta biya biliyoyin Naira ga mutanen da kudadensu suka makale sanadiyyar rufe bankunan.
- Burin Saudiyya Na Daukar Nauyin Gasar Kofin Duniya Na 2034 Na Gab Da Cika
- An Kammala Taron Tsaro Na Xiangshan Karo Na 10 Na Beijing
Aminu Hamisu, mataimakin manajan hukumar NDIC na shiyyar Bauchi, ya fayyace irin bankunan da rufewar ta shafa.
Ganin cewa, a jiya ne aka kaddamar da bikin ranar ajiya a banki a Duniya domin wayar da kan jama’a da kuma gabatar da kasidu a wuraren da aka gudanar da taruka don fadakar da mutane muhimmancin yin ajiya a bankin, Ajiya Bah Zarma, konturola na hukumar NDIC da ke shiyyar Bauchi, ya yi karin haske.
Taken ranar yin ajiya a bankin na wannan shekarar, shi ne: ‘ka nemi galaba akan yau dinka domin raya gobe’.
Ya ce da yawan bankunan da aka rufe sun shiga matsalolin da suka shafin tattalin arziki lamarin da bar hukumar da biyan makudan kudade da mayar wa mutane kudadensu da suke ajiya.
Ire-iren wadanann matsaloli su ne ke yi wa masu ajiya katutu a zuciya, wanda a wasu lokuta ke sanya wasu yanke shawarar ajiye kudadensu a gida.
A cewar hakan kuma na iya shafar tattalin arzikin tafiyar da harkokin bankuna, wanda shi ma na iya shafar tattalin arzikin kasa a wasu lokuta.