Ya zuwa yanzu hukumomi a Jihar Taraba sun tabbatar da mutuwar mutum 17 yayin da aka ceto mutum 14.
Kwale-kwalen da ya yi hatsari na dauke da ‘yan kasuwa da ke dawowa daga kasuwar kifi da ke gundumar Ardo-Kola ta jihar Taraba da yammacin ranar Asabar lokacin da ya kife a Kogin Benue, wanda shi ne daya daga cikin ruwa mafi girma a Nijeriya.
- Gwamna Lawal Ya Jagoranci Taron Majalisar Zartaswa Kan Tattara Kudin Fansho
- ‘Yansanda Sun Cafke Saurayin Budurwar Da Ta Mutu Yayin Jima’i A Kwara
Fiye da fasinjoji 100 ne ke cikin jirgin, sannan an ceto 14, yayin da aka gano gawarwaki mutane 17, amma kuma mutane 73 ne suka bace, kamar yadda shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, Ladan Ayuba, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN).
Gwamnan jihar Taraba Agbu Kefas ya kwatanta hatsarin a matsayin babban abin takaici kuma ya ba da umarnin amfani da rigunan ceto ga fasinjojin kwale-kwale.
“Ruwan kasarmu, wanda shi ne daya daga cikin mafi dadewa a yankin, ya kamata ya zama tushen arziki ne ba na mutuwa ba,” in ji gwamnan, a cewar wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
Iftila’in kifewar kwale-kwale na kara zama ruwan dare a tsakanin al’ummomi da ke yankunan karkara a a wasu jihohin Nijeriya.
Wannan shi ne hatsari na uku da ya shafi fasinjoji sama da 100 cikin watanni hudu kacal.
Yawanci ana danganta haduran da daukar kaya fiye da kima.
Babu hanyoyin mota masu inganci a ire-iren wadannan yankuna.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Taraba, Usman Abdullahi ya ce jami’an tsaro na gudanar da bincike don gano musabbabin faruwar wannan hatsarin.
Mazauna yankin da masunta suna taimaka wa hukumomin ceto don ganin an kubutar da wadanda lamarin ya rutsa da su.
Abdullahi ya ce yana fargabar cewa aikin binciken na iya daukar kwanaki kafin a kammala saboda kogin yana kan ganiyar tumbatsa.
“Ba ma tsammanin za mu samu gawarwakin a nan kusa,” in ji shi.