A ranar Laraba kotun daukaka kara da ke Abuja ta tsige tsohon gwamnan jihar Benuwe, Gabriel Suswam daga kan kujerar sanata.
A wani hukunci da kotun mai dauke da alkalai uku suka yanke, kotun daukaka kara ta bayyana cewa Suswam bai lashe zaben sanata da aka gudanar a Benuwe ta Arewa maso Gabas a ranar 25 ga watan Fabrairu ba.
- Shirin Tsige Fubara: Gwamnonin PDP Za Su Gana Da Wike A Abuja
- Bam Ya Yi Ajalin Mutane 20, Ya Jikkata 2 A Yobe
Kotun ta soki matakin da kotun sauraron kararrakin zabe ta Jihar Benuwe ta yanke na soke zaben Mista Emmanuel Udende na jam’iyyar APC wacce ta mayar da Suswam na PDP zuwa majalisar dattawa.
Kotun daukaka kara ta bayyana cewa, kotun sauraron kararrakin zaben ta yanke hukuncin da bai dace ba.
Sakamakon haka, kotun ta bayyana cewa, dan takarar APC shi ne ya lashe zaben, kuma ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben jihar da ta tabbatar da Suswam a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar Sanatan.