Sabon Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kebbi, Alhaji Faruk Musa Yaro Enabo, ya bai wa Gwamna Nasir Idris da al’ummar Jihar tabbacin gudanar da aikin Hajji nagari.
Shugaban ya nuna matukar godiya ga Gwamna Idris bisa samun sa da ya cancanci a nada shi a irin wannan matsayi mai girma, inda ya yi alkawarin sauke dimbin amanar da aka dora masa.
- Sojoji Sun Kashe Kasurgumin Kwamandan ‘Yan Bindiga A Kebbi
- Ku Yi Aiki Tukuru Ko Na Kore Ku, Tinubu Ga Ministoci
Shugaban hukumar ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar ragamar jagorancin hukumar a Birnin Kebbi, da kuma yin jawabi ga ma’aikatan hukumar da masu fatan alheri.
Shugaban ya gode wa Allah da ya ba shi wannan aiki na addini mai daraja, sannan ya sanya fata da amana, shi domin shiriya da taimako don sauke nauyin da ke kansa da matukar nasara.
Alhaji Faruk Musa ya bayyana sauran mambobin hukumar a matsayin fitattun mutane, inda ya ba da tabbacin cewa za su fara aiki nan take domin samun kyakkyawan aikin Hajji na aikin hajji mai zuwa.
Haka kuma ya yi bayanin tsarin bizar da kasar Saudiyya ta yi na aikin Hajjin shekarar 2024, inda ya bayyana cewa, sabanin abin da aka samu a baya na wahalar da ake fuskanta na ba da biza cikin kankanin lokaci, bayar da bizar ga maniyyata daga yanzu zai dogara ne kan biyan kudin aikin Hajji gaba daya.
Sai dai ya bayyana cewa da zarar duk wani mahajjaci ya biya kudinsa gaba daya, hukumomin kasar Saudiyya za su ba shi bizar, inda ya ce tuni aka bude hanyar shiga ta kuma za a rufe bayan mako uku.
Shugaban ya sanar da duk mai niyyar zuwa aikin Hajji cewa makonni biyu kacal a cikinsu su biya kudin aikin Hajjin da ya kai Naira miliyan 4.5 sannan ya bukace su da su gaggauta biya.
Tun da farko, a jawabin maraba Alhaji Sani Idris Abarshi, sakataren hukumar ya bayyana farin cikinsa da nadin Faruq Musa Yaro Enabo a matsayin shugabanta, inda ya bayyana shi a matsayin wanda ya kware da kwazo.
Alhaji Sani Abarshi, ya yaba wa Gwamna Nasir Idris bisa amincewa da Alhaji Faruk Musa wajen tafiyar da harkokin Hukumar Jin Dadin Alhazai, inda ya yi alkawarin ba shi dukkan goyon baya da hadin kai don samun nasara.
Cikin wadanda suka raka shugaban domin karbar ragamar mulki har da shugaban jam’iyyar APC na jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Muhammad Kana Zuru da dimbin masoya da abokan arziki.