• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Siyasar Ubangida: Baya Ta Haihu A Jihar Ribas

by Yusuf Shuaibu
2 years ago
Ribas

An samu takaddamar siyasa a garin Fatakwal, Babban Birnin Jihar Ribas, sakamakonn yunkurin tsige gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, da wasu ‘yan masalisar dokokin jihar suka yi, wadanda ake zargin masu biyya ne ga ministan Abuja, Nyesom Wike.

Lamarin ya yi tsami har sai da Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya shiga tsakanin rikicin siyasar Jihar Ribas da ta kunno kai.

  • Baje Kolin CIIE Na Kara Jan Hankalin Sassa Kasa Da Kasa
  • Zamu Sabanta Dakin Karatu Na Sashen Harsunan Nijeriya Na Jami’ar Bayero — Hassan Baita

Dangantaka dai ta yi tsami tsakanin Gwamna Fubara da wanda ya gada, Wike wanda a halin yanzu yake rike da mukamin ministan Babban Birnin Tarayya Abuja.

Siyasan ubangida yana matukar take muhimmiyar rawa a cikin siyasar Nijeriya, wanda wannan ba sabon al’amari ba ne a domin an samu irin wannan lamari a mafi yawancin jihohin kasar nan.

‘Yan siyasan Nijeriya sukan kokarin kafa yaransu a lokacin da wa’adin mulkinsu ya kusan shudewa tare da tsammanin yi musu biyya a gare su.

LABARAI MASU NASABA

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

Duk da hakan, wannan kokari kan dore a wasu lokuta, yayin da a wasu lokutan kuma ake yin baran-baran a tsakanin ubangida da yaronsa na siyasa.

Da wasu daga cikin ‘yan siyasan Nijeriya da suka raba gari a tsakanin ubangida da yaronsa na siyasa.

Nyesom Wike Da Rotimi Amaechi

Nyesom Wike da Rotimi Amaechi sun taba zama abokan juna. Inda Amaechi ya goyi bayan Wike na zama gwamnan Jihar Ribas. Sai dai alakar tasu ta wargaje a lokacin zaben 2015. Amaechi da gwamna mai ci sun mara wa Dakuku Peterside baya, a matsayin wanda zai gaje shi, yayin da Wike, tsohon shugaban ma’aikatan Amaechi, suka tsaya takara a karkashin tutar jam’iyyar PDP, kuma suka yi nasara. Wannan bambancin dai ya janyo zargin juna, inda Wike ya yi zargin cin hanci da rashawa a kan Amaechi da kuma sukar sa kan rashin kula da jin dadin jihar.

Godwin Obaseki Da Adams Oshiomhole

Godwin Obaseki da Adams Oshiomhole sun taba zama ubangida da yaro a Jihar Edo. Oshiomhole, tsohon gwamnan ya goyi bayan takarar Obaseki a matsayin wanda zai gaje shi. Sai dai kuma bayan da Obaseki ya hau kan karagar mulki, rikici ya kaure a tsakaninsu. Oshiomhole ya zargi Obaseki da rashin mutuntawa tare da yin watsi da mai gidansa, wanda hakan janyo yunkurin tsige Obaseki daga kujerar gwamnan Jihar Edo a 2020.

Abdullahi Ganduje Da Rabiu Kwankwaso

Abdullahi Ganduje da Rabiu Kwankwaso sun yi kawancen siyasa a Jihar Kano. Kwankwaso, tsohon gwamnan ya amince da Ganduje a matsayin wanda zai gaje shi. Sai dai alakarsu ta yi tsami ne bayan rantsar da Ganduje a matsayin gwamnan Jihar Kano. Kwankwaso ya zargin Ganduje da cin hanci da rashawa, ya kuma soki Ganduje da kin bin shawararsa, wanda hakan ya sa Kwankwaso ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP, daga baya kuma sa koma jam’iyyar NNPP.

Peter Obi Da Chris Ngige

Peter Obi da Chris Ngige sun taba zaman ubangida da yaro a siyasar a Jihar Anambra. Ngige ya kasance tsohon gwamnan, yayin da ya goyi bayan Obi a matsayin magajinsa. Sai dai kuma dangantar tasu ta tabarbare bayan Obi ya hau kan karagar mulki. Ngige ya zargi Obi da cin hanci da rashawa da rashin bin ubangidansa, wanda hakan ya sa Ngige ya fice daga PDP zuwa APC.

Bukola Saraki Da Shugabanin PDP Na Kwara

Bukola Saraki da jiga-jigan PDP na Jihar Kwara sun kasance abokan siyasa na kut da kut a baya. Shugabannin jam’iyyar PDP na Jihar Kwara, karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar, Sanata Shaaba Lafiagi, sun goyi bayan Saraki ya zama gwamna. Sai dai alakar bangarorin biyu ta yi tsami bayan rantsar da Saraki. Saraki ya zargi shugabannin jam’iyyar PDP na Jihar Kwara da cin hanci da rashawa da kuma kokarin shawo kansa ta hanyar da ba ta dace ba. Rikicin da barke tsakanin bangarorin biyu wanda ya kai ga ficewar Saraki daga PDP zuwa APC. Sai dai daga baya Saraki ya koma PDP.

Aminu Tambuwal Da Aliyu Wamakko

Aminu Tambuwal da Aliyu Wamakko sun taba zama ubangida da yaro a fagen siyasar Jihar Sakkwato. Wamakko wanda ya kasance tsohon gwamnan ya goyi bayan Tambuwal a matsayin wanda zai gaje shi. Sai dai dangantakarsu ta yi tsami bayan rantsar da Tambuwal a matsayin gwamna. Wamakko ya zargi Tambuwal da rashin mutunta ubangidansa. Wannan rashin jituwa ta sa Tambuwal ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC, inda daga baya koma.

Olusegun Mimiko Da Adebayo Adefarati

Olusegun Mimiko da Marigayi Adebayo Adefarati a baya sun kasance ubangida da yaron siyasa. Adefarati, tsohon gwamnan Jihar Ondo, ya goyi bayan Mimiko na neman kujerar gwamna. Duk da haka, dangantakarsu ta yi tsami bayan Mimiko ta hau kan karagar mulki na gwamnan Jihar Ondo. Adefarati ya yi zargin rashin mutuntawa da kuma yin watsi da shawararsa, wanda hakan ya haifar da sabani a tsakaninsu. Wannan rashin jituwa ya sa Adefarati ya sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta AD zuwa jam’iyyar PDP.

Daga cikin wadannan za ku iya fahimtar cewa rikicin siyasar da ke faruwa a yanzu tsakanin Nyesom Wike da Sim Fubara ba sabon abu bane a fagen siyasar Nijeriya. Haka nan ana iya lura da yanayin sauya sheka a tsakanin ‘yan siyasan Nijeriya sakamakon rashin jutuwa, sannan kuma za a iya hasashen yiwuwar maimaita irin wannan lamari a cikin ‘yan siyasar PDP na Jihar Ribas.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 
Manyan Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

October 9, 2025
SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati
Labarai

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba
Labarai

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Next Post
Rabon Tallafin Rage Radadi: Wane Hali Ake Ciki?

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

October 9, 2025
SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.