ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Za Mu Sabunta Ɗakin Karatu Na Sashen Harsunan Nijeriya Na Jami’ar Bayero — Hassan Baita

by Leadership Hausa
3 years ago
Jami'ar Bayero

Tsofaffin Ɗaliban Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe na Jami’ar Bayero ‘yan ajin shekarar karatu ta 2011 zuwa 2015 sun sha alwashin sabunta ɗakin karatu na sashen wanda aka fi sani da Ɗakin Karatu Na Farfesa MAZ Sani.

Shugaban tawagar tsofaffin ɗaliban, Alh. Hassan Baita Ubawaru, ne ya bayyana haka yayin da ya ke miƙa wasu sababbin injinan naɗar takardu (Photocopy) guda uku da ya gwangwaje sashen nasu a madadin ɗaliban a matsayin gudunmawarsu don sauƙaƙa harkokin koyo da koyarwa a sashen a ranar Alhamis 02, ga watan Nuwambar 2023.

Injinan Nadar Takardu Uku Da Tsofaffin Daliban Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya Suka Suka Ba BUK
Injinan Naɗar Takardu Uku Da Tsofaffin Ɗaliban Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya Suka Suka Ba BUK
  • Jami’ar Bayero Ta Sanar Da Ranar Bude Makaranta Don Ci Gaba Da Karatu
  • Tsohon Shugaban Jam’iar Bayero Ta Kano, Farfesa Ibrahim Umar Ya Rasu

Da yake miƙa injinan, Alh. Hassan Baita, wanda shi ne shugaban taron sada zumunci na ‘yan ajin shekarar 2015 kuma wanda ya ɗauki nauyan sayan injinan ya ce, wannan somun-taɓi ne kuma lokaci bayan lokaci za a ke irin waɗannan ayyuka don bunƙasa wannan sashe.

ADVERTISEMENT
Tsofaffin Daliban Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya Yayin Mika Injinan Nadar Takardu A BUK
Tsofaffin Ɗaliban Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya Yayin Miƙa Injinan Naɗar Takardu A BUK

A nasa jawabin, tsohon Sakataren Ƙungiyar Hausa ta Jami’ar Bayero, Muhammad Bashir Amin, ya bayyana ƙudurinsu na bunƙasa sashen ta hanyar bijiro da ayyukan da za su ciyar da sashen gaba, ya kuma buƙaci malamai da su ƙara kyautata alaƙarsu da ɗalibansu su ja su a jika, su ɗauke su tamkar ‘ya’yan da suka haifa, saboda hakan zai ƙara yi wa ɗaliban ƙaimi wajen tunawa da su bayan Allah ya ɗaukaka su a rayuwa.

Shugaban Sashen, Farfesa Isah Mukhtar, ya godewa ɗaliban da suka yi wannan hoɓɓasa da abun arziƙi a lokacin da ya ke shugabantar sashen, ya kuma bayyana cewa haƙiƙa irin wannan tallafi zai taimaka musu su tsallake tantancewar hukumar kula da Jami’o’i ta ƙasa da za ta yi wa sashen a shekara mai zuwa, wanda gaza samar da kayan koyo da koyarwa da kayan gudanar da aiki ka iya kaiwa ga samun babbar matsalar da zata iya kaiwa ga rufe sashen baki ɗaya.

LABARAI MASU NASABA

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 245, Ta Raba 214,997 Da Muhallansu A 2026 – NEMA

2027: Tinubu Zai Samu Ƙuri’u Masu Yawa A Kano – Gwamna Yusuf

Taron ya samu halartar mataimakin shugaban tsangayar fasaha da nazarin addinin musulunci da malaman sashen yayin bikin miƙa injinan.

Mahalarta taron daga ɓangaren malamai da ɗalibai sun jinjinawa ƙoƙarin tsofaffin ɗaliban na samar da injinan, sun kuma gode musu da fatan Allah ya yalwata arziƙinsu.

Jami'ar Bayero
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    PalmPay Na Ƙara Wayar Da Kan Jama’a Game Da Hanyoyin Tuntuɓar Tallafi Na Hukuma Yayin Da Haɗarin Zamba Ke Ƙaruwa
  • Leadership Hausa
    ‘Yan Nijeriya Sun Gaji Da Uzurin Gwamnati Na Ƙarin Farashin Mai A Ƙasa
  • Leadership Hausa
    Bukatar Guje Wa Siyasantar Da Matsalar Tsaro
  • Leadership Hausa
    Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar

MASU ALAKA

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 245, Ta Raba 214,997 Da Muhallansu A 2026 – NEMA
Manyan Labarai

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 245, Ta Raba 214,997 Da Muhallansu A 2026 – NEMA

October 24, 2026
Gwamnatin Kano Ta Rufe Asibitocin Kuɗi 35
Manyan Labarai

2027: Tinubu Zai Samu Ƙuri’u Masu Yawa A Kano – Gwamna Yusuf

October 23, 2026
Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe
Labarai

Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

October 23, 2026
Next Post
Yadda Rakiyar Gwamnan Kano Ga Tagwayen da ke Manne Da Juna Ta Dauki Hankalin Al’umma

Yadda Rakiyar Gwamnan Kano Ga Tagwayen da ke Manne Da Juna Ta Dauki Hankalin Al'umma

LABARAI MASU NASABA

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 245, Ta Raba 214,997 Da Muhallansu A 2026 – NEMA

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 245, Ta Raba 214,997 Da Muhallansu A 2026 – NEMA

October 24, 2026
Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo

Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo

October 23, 2026
Gwamnatin Kano Ta Rufe Asibitocin Kuɗi 35

2027: Tinubu Zai Samu Ƙuri’u Masu Yawa A Kano – Gwamna Yusuf

October 23, 2026
Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

October 23, 2026
Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

October 23, 2026
Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

October 23, 2026
NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

October 23, 2026
Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

October 23, 2026
Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

October 23, 2026
Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.