Wani mazaunin garin Jibiya da ke Jihar Katsina, Aminu Yusuf ya ba da labarin yadda matarsa, Malama Ladi, wacce ke shayar da jariri da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da ita, ta zabi ta yi shahada a maimakon bari daya daga cikin masu garkuwa ya tursasa mata aurenshi.
Matar wacce ta rasu a lokacin da dan bindigan ya yi kokarin kwanciyar aure da ita. Ta bi dukkanin matakan da suka dace wajen kin amince masa. Wani abun takaici ma shi ne, masu garkuwan sai da suka karbi kudin fansa da nufin za su saki matar, amma suka aikata mata wannan danyen aikin.
- Yadda Rakiyar Gwamnan Kano Ga Tagwayen da ke Manne Da Juna Ta Dauki Hankalin Al’umma
- Mutum Miliyan 2 Za Su Ci Gajiyar Tallafin Kiwon Lafiya A Bauchi
A wani sautin murya na tattaunawar da ta wakana tsakanin mijinta da daya daga cikin kwamandojin masu garkuwa da mutanen da aka yi ta yadawa a kafafen sadarwar zamani. An ji shugaban masu garkuwan na bayanin yadda daya daga cikin yaransa ya yi da wacce suka kaman, kuma da yadda shi Yusuf din ke rokon su dawo masa da gawar matar tasa.
A hirarsa da LEADERSHIP, Yusuf ya yi karin hasken abubuwan da suka wakana har suka janyo kashe masa mata, ya ce, tun lokacin da abun ya faru hankalinsa a tashe yake ko barci baya iyawa, duk kokarin da suka yi na ceto matar, amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba.
Lamarin ya faru ne a tsakanin Magama-Jibiya da ke karamar hukumar Jibiya a Jihar Katsina, abun ya tada hankalin jama’a da ba su mamaki matuka ganin yadda mutane ke gwagwarmayar tsira da rayuwarsu kan halin matsatsin tattalin arziki da ake ciki a kasar nan a halin yanzu.
Da jaridar LEADERSHIP ta ziyarci gidan Yusuf da ke Magama-Jibiya domin samun labarin rashin imani da zalumcin da ya samu matarsa. Ya ba da labarin yadda suka yi ta tattaunawa da shugaban masu garkuwa da mutanen domin ganin an samu daidaito kan kudin fansa, amma daga baya kuma lamarin ya gagara.
A cewarsa, shugaban masu garkuwan bayan da aka sace matarsa sun tuntubeshi ta wayar tarho, inda suka bukaci ya biyasu naira miliyan 10 a matsayin kudin fansar matarsa. Ya yi ta rokonsu cewa a rayuwarsa gabaki daya bai taba rike irin wannan kudin masu yawa ba.
Ya ce bayan kwanaki da tattaunawa da su, shugaban masu garkuwan ya rage kudin zuwa naira miliyan biyar, har suka cimma matsaya a kan naira miliyan biyu, amma iyaka abun da suka iya tarawa kawai shi ne naira dubu dari bakwai da wayoyin zamani manya guda uku da suka kai wa ‘yan bindigar.
“Shugaban masu garkuwan ya shaida min cewa zai yi tafiya zuwa wani wajen, amma na ci gaba da tattaunawa da yaronsa.
“Nan take na sayar da motata a kan kudi naira dubu dari biyar, sannan ina son na sayar da gidana amma ban samu mutumin da zai saya ba saboda halin matsalolin tattalin arzikin da ake ciki. Na samu damar harhada wasu ‘yan kudi kalilan daga abokai da ‘yan’uwa da makwafta. Gaba daya dai a takaice mun hada naira dubu dari bakwai da wayoyin ‘Andirol’ guda uku.
“Masu garkuwan sun amince cewa za su hadu da mu, mun kuma tattauna da surukata kan yadda za ta kai musu kudin. Ta amince kuma wannan shi ne hakikanin abun da muka tsara, saboda muna fargabar kar su sake cafke wani idan aka kai kudin.
“Ta kai musu kudin kuma sun yi alkawarin za su sake ta a washegari, amma abun takaici ba su yi hakan ba. Tun daga wannan lokaci wayarsu ba ta shiga.
“Bayan wasu ‘yan lokutan, na fara jin jita-jitan cewa ‘yan bindigan sun kashe matata. Sannan wata yarinya da aka yi garkuwa da ita ta tabbatar min da wannan daga baya. Sun kasance tare da matata a inda aka tsare su. A cewarta, matar tawa an tursasa mata yin aure da wani daga cikin masu garkuwan, a lokacin da ya yi kokarin kwanciya da ita, ta ki amincewa ta ba shi hadin kai, ta zabi ta rasa ranta da ta mika kanta da mutuncinta, hakan ya sanya ‘yan bindiga suka harbe ta da harsashi har sau biyu,” in ji shi.
Yusuf ya ce tun lokacin da suka tabbatar da kisan matar tasa, ya fadi ya suma, kuma a halin yanzu rayuwa ta masa kunci domin kula da ‘ya’ya biyu da suka haifa da matarsa.
“Matata ta rasu ta bar ‘ya’ya biyu, dayansu na farko shekaransa uku a duniya, kaninsa kuma shekaransa daya wanda a halin yanzu yana shan mama.
“Lokacin da ‘yan bindigan suka yi garkuwa da mamarsa, daya daga cikin yarona ya yi kokarin bin mahaifiyarsa, amma ta jajirce ta ce ka da ya biyo ta.”