Firaministan Burtaniya Boris Johnson ya yi murabus daga mukaminsa, wanda ya kawo karshen zamansa a firaministan tsawon shekaru uku da cece-kuce da badakala ta dabaibaye gwamnatinsa.
Da yake magana, Johnson ya ce ya kamata a fara shirye-shiryen zaben sabon shugaban jam’iyyar Conservative a yanzu, Sannan a bayyana jadawalin tsarin mako mai zuwa.
Yce zai cigaba da zama a ofis har sai an zabi sabon shugaban Jam’iyyar.
Tsohon Firaministan zai cigaba da zama a kan karagar mulki duk da rashin goyon bayan da jam’iyyarsa ke nuna masa da kuma kiraye-kiraye na ya sauka daga Mukaminsa Cikin gaggawa.
Johnson ya ce “ya yi bakin cikin barin mafi kyawun aikin da ya fiso a duniya,” amma ya yarda cewa “babu wanda ya gagara” a siyasa.