Mai shari’a Ramon Oshodi na kotun Kiyaye cin zarafi da laifukan kiyaye Hakkin Jinsi ta jihar Legas, ya yankewa wani malamin addinin Musulunci, Isa Mustapha dan shekara 50 hukuncin daurin rai-da-rai bisa laifin lalata da ‘yar makwabcinsa ‘yar shekara takwas.
Mai shari’a Oshodi ya tura Mustapha gidan yari har karshen rayuwarsa bayan da ya Tabbatar da cewa masu gabatar da kara sun yi nasara kan Wanda ake tuhuma.
Gwamnatin Jihar Legas ta gurfanar da Malamin a gaban Kotu bisa tuhuma daya da ake yi masa na lalata ‘yar makwacinsa da ya saba wa sashe na 137 na dokokin manyan laifuka na Jihar Legas, 2015.
A yayin shari’ar, mai gabatar da kara ya gabatar da shaidu hudu yayin da wanda ake tuhuma ya bayar da shaida a kan kare kansa.