Alkalin wasa dan kasar Ingila, Anthony Taylor, ya koma alkalancin gasa mai daraja ta biyu ta ‘Championship’ bayan tafka kuskure a wani wasan da ya jagoranta.
Bayan korafe-korafe da dama akan Taylor kan yadda yake gudanar da alkalanci, hukumar kwallo ta kasar Ingila (FA), ta same shi da tafka kuskure a wasan da aka buga tsakanin Wolves da Newcastle.
Hakan ya sa hukumar Ingila ta mayar da shi gasar ‘yan dagaji wanda zai fara da wasan Coventry da Preston End a wannan satin.