DAKTA AWWAL ABDULLAHI ALIYU, Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Kare Hakkokin ‘Yan Arewa ta Kasa (Northern Consensus Mobement), wadda ke da kungiyoyi sama da 500 daga jihohi 19 na Arewacin Nijeriya, wadanda suke magana da murya daya a kan al’amuran da suka shafi Arewa, ya bayyana ra’ayinsa kan cewa; muddin ana bukatar shawo kan matsalar tsaron da ta addabi Arewacin Nijeriya, wajibi ne a samar da hadin kai tsakanin al’umma da jami’an tsaro wajen bayar da bayanan sirri. A zantawarsa wakilanmu, SHEHU YAHAYA a ofishinsa da ke Kaduna, ya nuna rashin amincewarsu dangane da matakin da Gwamnan Jihar Katsina ya dauka na cewa al’ummar jihar su dauki bindiga, domin kare kansu daga harin ‘yan ta’addan da suka addabi jihar. Ga dai yadda hirar tasu ta kasance:
Har yanzu yankin Arewa na fama barazanar rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki, wadanne irin matakai kuke dauka domin ceto yankin?
Ko shakka babu, duk inda muka ga akwai matsalar tsaro mukan fito mu yi bayani cewa, akwai wannan matsala a wuri kaza da wuri kaza, sannan mu aika wa duk hukumomin da suka kamata; wato dukkanin jami’an tsaron kasar nan a rubuce duk da cewa, mun san sun sani; amma mukan kaddara cewa ba su sani ba, amma mun san sun sani.
Haka nan, duk wani wanda muka san mai fada a ji ne a kasar nan, kama daga shugaban kasa da tsoffin shugabannin kasa da gwamnoni da kuma majalisar dattawa da ta wakilai da sauransu, duk mu kan sanar da su halin da ake ciki, sannan mu ba da shawara cewa; idan an yi kaza za a samu mafita. Ba ma tsayawa iya nan, har sai mun garzaya kafafen yada labarai irin naku mun sanar da al’umma irin halin da Arewa take ciki, wannan kenan domin samo bakin zaren.
Sannan, mukan shirya taro mu kira manyan mutane da masana mu zo mu zauna, mu dubi matsalar tsaron da kanta sannan mu fito da hanyoyin da za a warware su. Kwanakin baya, mun shirya wani taron koli ga Fulani, inda muka kira shi da ‘Fulbe Fulani Summit’, wanda shi ne irinsa na farko a Nijeriya, inda muka tara su hardodin fulani da suke fadin Nijeriya da kuma Sarakunan Fulani da ke Kasashen Afirka guda bakwai da suka hada da Ghana, Burkino Faso, Benin, Mali, Chadi, Kamaru da Sierra Leone, muka yi taro da su a Abuja tare da Gwamnonin Arewa guda bakwai da mai ba wa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, duk sun halarci wannan taro da kuma wakilan shugannin tsaro.
Har ila yau, mun shirya taron ne domin gano musabbabin matsalar Fulani tare da sanin hanyar da za a bi wajen shawo kan matsalar, duk da cewa mun yi nasarar samun wadannan bayanai masu inganci a kan matsalar.
Shi kansa babban bako mai jawabi, Tsohon Hafsan Tsaron Nijeriya, Abdulrahman Danbazau; ya fito da gundarin bayani a kan tsaron kama daga matsalar tsaron da kuma wadanda ake ganin su ne ke kawo matsalar tsaron, wato Fulani da yadda za a magance matsalolin. A kan hakan ne muke cewa Fulani, yanzu fa kule a gare ku, ya zama wajibi a zauna a ga yadda za a magance wadannan matsaloli da shi Danbazau din ya zayyana. Sannan bayan taron, mun tura wa hukumomin tsaron kasar nan; ciki har da fadar shugaban kasa a kan shawarwarin da aka bayar kan yadda za a magance matsalolin tsaron a yankunan Arewa.
Haka zalika, idan muka dawo bangaren harkokin tattalin arziki kuma, abin da muka a sani a Arewa shi ne, harkar noma da kiwo wadanda su ne abin da aka san dan Arewa da shi kenan. Kamar yadda ka sani dai, waccan matsalar ta tsaro ita ce dai take kara kawo koma baya a kan tattalin arziki, domin kuwa ta hana manoma su je su yi noman, sannan kuma ta hana wadanda ba makiyaya ba kiwo.
Noma shi ne jigon tattalin arziki, domin kuwa sai an noma za a kai kasuwa a sayar, haka idan aka kiwata za a kai kasuwa a sayar, sai gashi wannan matsala ta tsaro ta hana kasuwanci; wanda wannan ba karamar illa ba ce babba.
A taron namu, kungiyarmu ta fito da matsalar noma da kiwo da ilimi da kuma harkar lafiya, wanda duk matsalar tsaron ya yi sanadiyyar cakudawa, ya hana Gwamnatocin Arewa motsi; ita kuma gwamnatin tarayya ta ce, tana yin bakin kokarinta. Su kuma mutane a can kasa, suna ganin kamar babu abin da ake yi.
Kamar dai yadda na fada cewa, mu a namu bangaren muna iya yin bakin kokarinmu na wayar da kan al’umma, irin hanyoyin da za a bi wajen shawo kan matsalolin tsaron da ya addabi Arewa.
Gwamnan Jihar Katsina ya ayyana cewa, lokaci ya yi da al’umma za su dauki bindiga don kare kansu daga harin ‘yan ta’adda. Shin kana ganin irin wannan mataki zai taimaka wajen shawo kan matsalar tsaron?
Gaskiya fisabilillahi, mu ba mu yarda da wannan tsari na cewa, al’umma su mallaki bindiga ba, idan ka ce kowa ya mallaki bindiga; ka ga kenan ka hada da mutumin kirki da na banza da kuma wanda zai mallake ta domin kare kansa da wanda zai mallake ta domin kwacewa jama’a halaliyarsu, ka ga kenan akwai matsala babba.
Eh! Na gamsu a matsayinsa na shi gwamna, wanda ya yi rantsuwa zai kare rayuka da dukiyoyin al’umma, yana da wannan fishi da damuwa a kan yadda ake kwashe dukiyoyin mutane, ake yi wa mata fyade da dai sauran makamantansu. Idan ka ji gwamna ya yi irin wannan magana, za a iya yi masa uzuri; domin wani nauyi ne a matsayin sa na gwamna yake neman ya sauke, amma dokar kasa ba ta sahale wa kowanne dan kasa ya mallaki bindiga ba.
Tsohon Gwamnan Katsina Masari, shi ma ya taba yin irin wannan magana cewa, kowanne Bakatsine ya mallaki bindiga, domin bai wa kansa kariya. A nan gaskiyar magana ita ce, dokar kasa ba ta yarda ba, kuma gwamna ba shi da hurumin sahale wa mutane mallakar bindiga ko makami, domin hurumi ne na gwamnatin tarayya. Alal misali, Gwamna Radda ya kaddamar da ‘yan sa kai, wadanda za su taimaka wa jami’an tsaron jihar, sannan kuma an ba su bindigar harba ka ruga, amma dai Masari shi ya fara aikin. Sai dai mu babban abin jin dadinmu shi ne, wani gwamnan ya fara aiki; wanda ya gaje shi ya ci gaba. Ka ga indai za a ci gaba da irin wannan tsari a Nijeriya, za a samu ci gaba sosai saboda abu ne mai kyau.
A matsayinku na jagororin kungiyoyin Arewa, me kuke gani a matsayin mafitar wadannan matsaloli, musamma a bangaren tsaro a halin yanzu?
Gaskiyar magana ita ce, abubuwa guda uku suna da matukar muhimmaci a cikin wannan tsari. Abu na farko shi ne, aiki tsakanin al’umma da jami’an tsaro, saboda jami’an tsaro su kadai ba za su iya magance matsalar tsaro ba, domin kuwa su ma mutane kamar kowa, bambancin kadai na horo ne da dabarun kisa a lokacin yaki da suka samu, amma su ma mutane ne kamar kowa, sannan suna da cikakken bayanin sirri; wanda shi ne zai taimaka musu, domin cimma nasara.
Misali, sai ya zama akwai wasu gungun mutane suna taro kuma taron ana kyautata zaton zai iya haifar da matsalar tsaro, sai a sanar da jami’an tsaro a cikin sirri su zo su kama wadannan mutane cikin sirri, to ka ga idan za a samu bayanai na sirri ga jami’an tsaron zai rage matsalar tsaro matuka. Saboda haka, wajibi ne sai an samu hadin kai tsakanin al’umma da jami’an muddin ana san magance matsalar.
Abu na biyu kuma shi ne, muna da karancin jami’an tsaro saboda jami’an tsaron da muke da su yanzu ba za su iya warware matsalolin tsaron da muke fama da shi ba. Akalla muna da mutane a Nijeriya sama da miliyan 200, sannan idan ka hada dukkanin jami’an tsaron Nijeriyar; ba su kai miliyan biyu ba, kenan akwai matsala.
Don haka, ya kamata a ce jami’an ‘yansanda kawai muna da akalla miliyan uku da wani abu, soja miliyan biyu; jami’an hukumar farin kaya miliyan biyu; jami’an fasa kwauri da na shige da fice miliyan daya-daya, sai ya zama idan ka dunkule su dukkanin su ba su, ba su haura miliyan biyu ba. Saboda haka, muna kira ga gwamnati ta ba da damar daukar ayyuka ga jami’an tsaro kuma a dauke su da yawa, a ba su kayan aiki na zamani tare da inganta rayuwarsu.
Mene ne sakonka ga al’ummar Arewa baki-daya?
Na farko dai, ya zama wajibi ga daukacin matasan Arewacin Nijeriya, su zama masu bin doka da umarni; su kuma kauce wa saba wa dokar kasa, saboda dokar kasa ba karya ba ce. Sannan kuma, a yi biyayya ga shugabanni tare da yi musu addu’a, ba tsinuwa ba, domin kuwa duk lokacin da ka tsine musu, kanka tsinuwar za ta dawo. Saboda haka, muna kira ga jagororin Arewa, musamma wadanda al’umma suka zaba; su sani cewa akwai hakkin al’umma akansu, wanda Allah zai tambaye su na kare dukiyoyinsu da rayuwarsu a duk inda suka samu kansu.