Nnewi a jihar Anambra ta sake cimma wata gagarumar nasara a bangaren kirkire-kirkire, inda a ranar 2 ga watan Oktoban 2023 wani dalibinta, dan shekara 28 a duniya, Ibelo Chinemerem, haifaffen garin Akokwa ta jihar Ima ya bai wa kowani da ke yankin mamaki ta hanyar kera jirgi da ya yi tafiya mai nisa a sama kuma ya shafe tsawon mintina bakwai kafin daga bisani ya sauko lami-lafiya.
Wannan abin ban mamakin ya faru ne a filin DCC da ke kusa da babban shataletalen Okpu-na-Egwu da ke kusa da tashar motocin kabu-kabu ta Eastern Mass Transit.
- Mi’ara Koma Baya-Taylor Ya Koma Alkalancin Gasar ‘Yan Dagaji Ta Kasar Ingila
- Sojoji Sun Ceto Masu Yi Wa Kasa Hidima 2 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Katsina
Chinemerem, wanda ya kammala sakandarin fasaha ta Akokwa, ya ce, ya fara yunkurin kera jirgi ne tun a shekarar 2014 lokacin yana makaranta amma ya bar makarantar a 2016, sannan sakamakon rashin kudin da zai shiga jami’a domin cigaba da harkokin karatunsa, nan ya yanke shawarar komawa Nnewi a shekarar 2016.
Ya ce, a shekarar 2014 ne ya kera jirginsa na farko, amma jirgin bai tashi sama ba balle ya yi yawo saboda karancin kayayyakin da ya yi amfani da su wajen hadawa.
“Na kera wancan din da Zink, amma kwata-kwata bai tashi sama ba,” ya shaida.
Ya kara da cewa, ya fara cimma nasarara a rayuwarsa ne a Nnewi a shekarar 2020 lokacin da ya samu gagarumin nasarar kera wani jirgi amma a yunkurin tashinsa ya fado ya yi hatsari nan take ya wargaje.
Ya ce, hakan bai sanya ya ji sanyin guiwa ba, hakan ya sake ba shi kwarin guiwa ma har ya sake hada wani a shekarar 2021 da ya tashi har ya yi yawo na tsawon mintina biyu, kuma ya sauko lami-lafiya ba tare da wani matsala ba. Ya kara da cewa, sunan jirgin ‘Cessla’.
Chinemerem, da ke da zama a Uru-Umudim Nnewi, ya shaida cewar ya fara kera babban jirginsa mai suna Biper Tube wata guda da ya wuce.
Ya jero sunayen kayan da ya yi amfani da su wajen hada sabon jirgin nasa da ya daukaki lifafarsa, da cewa, “Na yi amfani da DC na mota, propeller, giya, mai, kumfa, giyan sauka, batiri, mai damar aiki na 2200mah, da zai iya tsawon mintina shida ko bakwai a sama na shawagi.
“Na fara gwagwarmayar hada jirgi ne tun ina dan shekara goma a duniya.
Amma ban taba shiga cikin jirgin ba sai yanzu, ko filin jirgi ma ban taba shiga ba. Kawai ina kallon jirgi ne a talabijin yayin da ke shawagi
a sama.” Chinemerem, ya ce, a halin yanzu haka shi ma’aikacin wucin gadi ne a inda yake aiki domin samun taso sisi domin rufa wa kansa asiri. Ya kara da cewa yana aiki ne a wurin gine-gine, inda daga cikin aikinsa akwai dankan siminti da buluk domin a yi gini da su kuma a biyashi kudin kwadagonsa.
Ya ce, idan da zai samu wadataccen horo da kayayyakin aiki da yake bukata, tabbas zai iya gina jirgin saman da zai yi yawo da shawagi a fadin duniya kuma ya dawo inda ake so lami lafiya.
Ya bayar da bayanin shirinsa na cewa duk da fama da rashin wadataccen kudi, zai cigaba da kere-kere da hada abubuwa musamman jirage domin cimma burin rayuwarsa, ya bada tabbacin cewa idan da zai samu gudunmawar kayan aiki da abubuwan da suka dace zai hada jiragen da za a sha mamakinsu matuka.
Ya yi kira ga masu hannu da shuni da gwamnatoci da su ke taimaka wa matune irinsa masu kaifin basira da baiwa domin su samu damar cimma burikansu na rayuwa.