Masana sun ce, lokaci ya yi da Nijeriya za ta rungumi harkokin fasaha fiye da yadda take yi a da baya domin habaka tattalin arzikin kasar.
Da suke magana a wajen wani babban taron da aka shirya kan kimiyya mai taken damarmakin da suke bangaren kirkire-kirkire da cin gajiyarsu a Afrika da ya gudana a kwalejin kimiyya ta Yaba, wani kwararre a bangaren Microsoft a Nijeriya, Rowland Joseph, ya ce, bai wa harkar fasaha dama zai taimaka wajen jagorantar habakawa da bunkasar tattalin arziki, kuma mata da ‘yan Nijeriya da dama za su ci gajiyar shiga a dama da su.
- Mi’ara Koma Baya-Taylor Ya Koma Alkalancin Gasar ‘Yan Dagaji Ta Kasar Ingila
- Sharhi: Lokaci Ya Yi Da Tinubu Zai Fuskanci Matsalolin Nijeriya
Tsohon kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar Legas, Hakeem Popoola, ya lura kan cewa, zuwa yanzu a yadda ‘yan Nijeriya ke rungumar fasaha hakan na janyo tagomashi ga tattalin arziki, sai ya ce, idan aka kara azama za a cimma nasara fiye da yadda ake tunani.
Popoola, kayan gine-gine sun yi matukar tsada, yana mai cewa rungumar harkar fahasa, zai bai wa mutum damar amfani da wayarsa ko kwamfutarsa wajen gudanar da harkokin kasuwanci maimakon gina cibiyar sayar da data da ginin ke da tsada ga jama’a.
Ya kara da cewa, “Idan ka kalli cigaban Afrika, musamman tsakanin masu farawa, za su iya gudanar da ayyukansu da dama ta yanar gizo, wanda hakan zai taimaka sosai a samu cigaba. Za su iya samar da manhajoji na amfani da fasaha da zai taimakesu matuka. Hakan zai yi matukar taimakawa zai kuma bada damar samun cigaba mai habakuwa a Afrika.
“Idan ka kalli adadin cibiyoyin sayar da data da ake da su a Nijeriya, suna karuwa matuka, kuma muna da babban cibiyar data a Afrika. Microsoft ita ma taan da manyan cibiyoyi a Afrika ta Kudu. Kazalika, Google, tana da babban cable dinta a Nijeriya, wanda ke bayar da damar samun dimbin data da ke shigowa da fita cikin kasar. Muna kallon hakan a matsayin gagarumin cigaba ga fasaha. Kuma yanayin zai cigaba da fabaka. Na yi farin ciki sosai da cewa daliban kwalejin kimiyya ta Yaba suna runguma da koyon harkokin fasaha sosai,” ya shaida.