Wasu gungun ‘yan ta’addan da ake zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne, a ranar Lahadi, sun kai wani mummunar hari kan manoman shinkafa da ke yankin Zabarmari a lokacin da suke aikin noman shinkafa a karamar hukumar Mafa ta jihar Borno, inda suka kashe sama da mutum 15.
Wani manomin shinkafa, Awali Casa, ya tabbatar wa jaridar LEADERSHIP cewa, harin da aka kai ya sanya fargaba a zukatan manoman yankin na Zabarmari.
- Jiragen NAF Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Da Lalata Baburansu 40 Da Bindigu 6 A Borno
- Sojoji Sun Yi Ruwan Wuta Kan ‘Yan Ta’adda, Sun Halaka 160 A Borno Da Yobe
Awali ya ce, yanzu haka ana ci gaba da neman gawarwakin manoman da ‘yan ta’addar suka halaka a gonakinsu na shinkafa, an kuma laluben sauran mutanen da suka bace yayin kai harin.
LEADERSHIP ta rawaito cewa ‘yan ta’addar dauke da muggan makamai sun kai harin ne kan gonakin inda suka nufi manoman shinkafa da suke aikin girbi a kauyukan Koshebe da Karkut da Bulabulin da ke karamar hukumar Mafa ta jihar Borno, yankin ke da tazarar kilomita 20 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Wani masani kan yaki da ‘yan tayar da kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya ce ‘yan ta’addar sun kai harin ne kan babura inda suka raba kawunansu gida uku kafin su kai hari kan manoman.
Wannan majiyar ta ce ‘yan ta’addar ba su yi amfani da bindigu ba, sai dai sun yi amfani da wukake inda suka yi wa manoman yankan rago da sassara su.
“An gano akalla gawarwaki tara har zuwa daren ranar Lahadi, yayin da ake ci gaba da neman wasu da suka yi gudun tsira da ransu daga harin ‘yan ta’addar,” cewar Makama.
Idan dai za a iya tunawa ‘yan ta’addar Boko Haram a shekaru uku da suka gabata sun kashe manoman shinkafa sama da 76 a kauyen Zabarmari da ke karamar hukumar Jere a jihar.
Harin da aka da ‘yan ta’addar suka kai na bayannan sun ce sun kashe manoman shinkafa da dama, kuma yana a matsayin jan kunne ga manoman da kuma rundunar sojojin Nijeriya.