An kashe mutane da dama da suka hada da mata da kananan yara yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan masu yin Maulidi a kauyen Kusa da ke karamar hukumar Musawa a jihar Katsina.
Kimanin mutane 18 ne lamarin ya rutsa da su yayin da aka akai wasu da dama Asibitin Kashi (Orthopedic) na Katsina domin zare harsashen bindiga da ke jikinsu, yayin da wasu kuma aka kwantar da su a babban asibitin Musawa.
- Yadda Aka Gudanar Da Gasar Adabi karo Na Uku Don Bunƙasa Ilimin ‘Ya’ya Mata A Katsina
- ‘Yan ta’adda Sun Kashe Monoman Shinkafa 15, Da Tarwatsa Wasu Da Dama A Jihar Borno
‘Yan bindigar sun bude wuta kan masu Maulidin ne da misalin karfe 11:05 na dare na ranar Lahadi, inda kuma suka yi awon gaba da mutane da dama daga wurin taron.
An ruwaito cewa, kafin isowar jami’an tsaro, maharan sun arce daga wurin.
Da yake tabbatar da rahoton ga manema labarai, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce adadin wadanda abin ya shafa ya kai 18.