Lauyoyin hambararen shugaban Jamhuriyar Nijar, Bazoum Mohammed sun bukaci kotun ECOWAS da ke zama a Nijeriya da ta mayar da shi kan karagar mulki, yayin da suka shaida mata cewar hambarar da shi da kuma tsare shi take hakkinsa ne na bil Adama.
Wannan ya biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa zababben shugaban a ranar 26 ga watan Yuli tare da kuma tsare shi, saboda abin da suka kira gazawarsa ta samar da tsaro a fadin kasar da ke fuskantar matsalolin ‘yan ta’adda.
- Bashin Da Ake Bin Nijeriya Ya Haura Tiriliyan N89.3
- Gobara Ta Tashi A Shagon Sayar Da Kayan Kamfanin Samsung A Abuja
Lauyoyin shugaban sun gabatar da hujjojinsu da kuma bukatar amincewar kotun ta ECOWAS da ta mayar da Bazoum kan karagar mulki, duk da yake kasashe da dama basa mutunta umarninta.
Daya daga cikin lauyoyin tsohon shugaban, Seydou Diagne ya shaida wa kotun cewar juyin mulkin da aka yi wa zababbiyar gwamnati take hakkin bil Adama ne.
Lauyan wanda ya yi wa kotun bayani ta bidiyo daga mazauninsa da ke Senegal, ya bukaci sakin Bazoum ba tare da gindaya sharidodi ba, yayin da ya kuma soki tsare uwargidansa da kuma dansa.
Lauyar da ke kare gwamnatin sojin Nijar, Aissatou Zada ta shaida wa kotun cewar ba a taka doka ba wajen tsare shugaba Bazoum, saboda an killace shi ne a gidansa domin kare lafiyarsa, kuma iyalansa na iya zuwa ganinsa lokacin da suke so.
Sai dai lauyoyin Bazoum sun ce tun daga ranar 20 ga watan Oktoba sun kasa magana da shi, bayan da sojoji suka yi zargin cewar yayi kokarin barin kasar.
Kotun ta sanya ranar 30 ga watan nan a matsayin ranar yanke hukunci a kan shari’ar.