Tsohon babban mataimaki na musamman na tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, Dr Doyin Okupe, a ranar Alhamis, ya janye daga marawa takarar Peter Obi na jam’iyyar Labour baya.
Sakamakon haka, jam’iyyar Labour za ta sanar da sabon abokin takarar shugaban kasa a zaben 2023.
- Maganar Hadewar Kwankwaso Da Peter Obi Ta Rushe
- Kwankwaso Ka Da Ka Kuskura Ka Sake Alakantamu Da Peter Obi —Kungiyar IPOB
Dokta Okupe ya bayyana hakan ne ta shafin sa na Twitter da aka tabbatar a ranar Alhamis, inda ya ce ya mika takardar janyewa ga hukumar zabe ta kasa (INEC).
Ya rubuta: “A yammacin yau na mika wa INEC takardar janyewa daga mukamin mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour.
“Shugaban jam’iyyar na kasa zai sanar da wanda zai maye gurbinsa nan ba da jimawa ba. Ina matukar farin ciki da kasancewa cikin ‘yan gaba wajen samun nasarar jam’iyyar Labour.”
Idan zaku tuna cewa, Peter Obi a ranar 16 ga watan Yuni ya mayarwa INEC fom din takararsa da aka kammala da sunan Dr Okupe a matsayin abokin takararsa.
An yi hakan ne bisa bin dokar zabe ta 2022 da kuma ka’idojin INEC na ranar 17 ga watan Yuni domin mika sunayen ‘yan takara.
Kamar yadda dokar zabe ta tanada, jam’iyyar siyasa ba za ta iya maye gurbin dan takarar da aka tsayar da shi ba sai a lokuta biyu; idan wanda aka zaba ya mutu ko kuma idan wanda aka zaba ya janye daga takarar.
Sai dai kuma dangane da janyewar, wanda aka zaba yana da hurumin rubuta wasika ga jam’iyyar siyasar da ta tsayar da shi, wanda ke nuna cewa ya janye daga takarar, wanda kuma dole ne ya kasance tare da takardar shaidar da dan takarar ya rantse.