Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna, ta yi kira ga malaman addinin Musulunci da su taimaka wajen wayar da kan duk wasu maniyyata aikin Hajji kan bukatar gaggauta biyan kudaden ajiya don cika wa’adin ranar 31 ga Disamba, 2023.
Babban sakataren hukumar, Dokta Yusuf Yakubu Arrigasiyyu, ya bayyana cewa hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta tsayar da wa’adin watan Disamba a matsayin ranar karshe na rijistar maniyyata aikin hajjin 2024.
- An Kwace Kambun Hilda Baci A Gasar Dafa Abinci Ta Duniya
- Neja Na Neman Kaso 13 Na Kudaden Lantarki Da Ake Samu Daga Ruwa A Yankinta
Dokta Arigasiyyu ya yi wannan roko ne a yayin wani taron wayar da kan al’umma da aka shirya wa limamai da malamai daga gundumomi yankin 23 da aka gudanar a kananan hukumomin Kaduna da Sabon Gari a jiya.
A cewarsa, za a aike da kudin aikin Hajjin maniyyatan zuwa NAHCON a ranar 31 ga watan Disamba, 2023, domin bai wa hukumar damar shirin aikin Hajjin badi yadda ya dace.
Dokta Alrigasiyyu ya ce ma’anar wannan tsari shi ne shigar da dukkan limaman masallatan Juma’a na jihar domin su ne masu ruwa da tsaki a harkokin Hajji.
Sakataren zartarwa ya yi nuni da cewa limamai sun fi kusanci da maniyyata, don haka akwai bukatar a musu bayani game da wa’adin da aka ware don jan hankalin jama’a.
Ya ce bisa sabbin ka’idojin, bayar da biza zai fara ne watanni biyu kafin gudanar da aikin Hajji, sakamakom sauyi da kasar Saudiyya ta yi a kalandar tsarin aikin hajji.
Dokta Arigasiyyu ya bayyana cewa saboda wannan sauyi ya sa ake bukatar dukkan maniyyata su yi biya kudinsu kafin karshen wa’adin watan Disamba.
A nasa jawabin mukaddashin shugaban ayyuka na hukumar, Alhaji Abubakar Yusuf ya ce hukumar za ta ci gaba da hada kai da malamai wajen wayar da kan dukkan maniyyatan game da sabbin tsare-tsare da NAHCON da na Saudiyya suka bullo da su na sauya fasalin aikin Hajji.