A ranar Talatar da ta gabata, Majalisar Dattawa ta bukaci Gwamnatin Nijeriya da ta gaggauta daukar matakai tare da hadin gwiwa da wasu kasashe domin kawo karshen yakin da Isra’ila da Hamas ke ci gaba da yi domin ceton rayuka da dukiyoyi.
Haka kuma majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta matsa lamba don ganin an samar da kasashe biyu a yankin, a matsayin wani kuduri na din-din-din kan rikicin Isra’ila da Falasdinu kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shi, tun farko.
- Kasar Sin Za Ta Ci Gaba Da Yin Iyakar Kokarin Saukaka Rikicin Gaza
- Ministan Wajen Sin Ya Yi Kira Da A Tsagaita Wuta A Gaza
Wannan na kunshe ne a cikin kudurorin da Sanata Kawu Sumaila daga Jihar Kano ya gabatar.
Sumaila, Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu da wasu sanatoci 28 ne suka goyi bayan kudirin. Tun lokacin da rikicin ya barke a watan Oktoba, an kashe dubban mutane, da suka hada da mata, yara, da ma’aikatan agaji, yayin da aka jefa bama-bamai a gine-gine, makarantu, wuraren kiwon lafiya, da wuraren ibada.
Dangane da batun samar da mafita kan kafa kasashen biyu, sun bukaci a kafa guda daya daga bangaren Isra’ila.
Sanata Adamu Aliero na PDP, daga Jihar Kebbi, wanda ya bayar da gudunmawa a muhawarar da aka yi kan kudirin, ya ce, hasarar rayukan da aka yi a yakin da ake yi abu ne mai ban tsoro, kuma idan ba a kawo karshensa ba zai iya bazuwa ya zama yakin duniya na uku.
Da yake tsokaci kan kalaman Majalisar Dinkin Duniya, Kawu, a cikin kudirin, ya ce tun bayan barkewar rikicin na baya-bayan nan a watan Oktoba, an lalata wuraren ibada 18, tare da lalata gidaje 22,600, cibiyoyin kiwon lafiya 19, cibiyoyin ilimi 90, cibiyoyin masana’antu 70 wadanda Falazdiwa suka dogara da su.