Wata kotun daukaka kara da ke Abuja, ta sanar da ranar da za ta yanke hukunci kan karar da dan takarar kujerar gwamna karkashin jam’iyyar SDP Dakta Umar Ardo, ya shigar yana kalubalantar hukuncin kotun sauraren kararrakin zabe.Â
Kotun baya da ta saurari bukatar da Dakta Umar Ardo, mataimakinsa Amos Yusuf da jam’iyyar SDP suka shigar, ta sanar da ranar za ta yanke hukuncin, alkalin kotun ya ce kotu za ta sanar da bangarorin ranar hukuncin.
- Bikin Baje Kolin CIIE: Kasashen Afirka Kar Ku Yarda A Bar Ku A Baya
- Kwastam Ta Kwace Tirelar Shinkafa 13 Da Kayan Naira Bilyan 1.2
Da ma dai dan takarar kujerar gwamnan SDP Dakta Umar Ardo, ya kalubalanci da kotun sauraren koke-koken zabe ta yanke, inda ya yi watsi da kalubalantar nasarar lashe zaben da gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, INEC da wasu 16.
Da ta ke yanke hukuncin ranar 02/10/2023, shugabar tawagar alkalan kotun sauraren sauraren zaben mai Shari’a Theodora Uloho, ta yi watsi da koken bisa rashin cancanta.
Ta ce “takardar karar ba ta dace ba kuma ba a shigar da ita yadda ya kamata a gaban kotun ba, masu gabatar da kara ba su da tabbacin abin da suke bukata,”in ji ta.
Kan haka kotun ta tabbatar da nasarar gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, ta kuma ci tarar dan takarar kujerar gwamnan jam’iyyar SDP Dakta Umar Ardo Naira Dubu dari biyu (N200,000).
Wannan yasa Dakta Umar Ardo ya daukaka kara yana neman kotu ta yi watsi da hukuncin kotun sauraren kararrakin zabe.