Kotun kolin masana’antu ta kasa ta haramta wa kungiyoyin kwadago ta Nijeriya (NLC) da (TUC) da sauran kungiyoyi shiga duk wani yajin aiki.
Kungiyoyin sun bayyana cewa bayan wani taron majalisar zartarwa na kasa da aka gudanar a ranar Talata a Abuja, sun ayyana yajin aikin gama gari daga ranar 14 ga Nuwamba, 2023.
- Kotun Daukaka Kara Ta Sa Ranar Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Adamawa
- Bikin Baje Kolin CIIE: Kasashen Afirka Kar Ku Yarda A Bar Ku A Baya
Kungiyoyin sun dauki matakin ne biyo bayan cin zarafin shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero a jihar Imo.
Sai dai Gwamnatin Tarayya da Babban Lauyan Tarayya, da Ministan Shari’a sun shigar da kara a gaban kotu, inda suka roki kotun da ta dakatar da kungiyoyin daga shiga yajin aikin da suka shirya.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Benedict Kanyip ya umarci kungiyoyin kwadago da su dakatar da yajin aikin da suke shirya yi a fadin kasar nan.