Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa, gwamnatinsa za ta ci gaba da bayar da fifiko ga manyan makarantu, musamman domin a rinka yaye daliban da za su samu ilimin zamani mai inganci da zai yi daidai da na fadin duniya.
Tinubu ya sanar a hakan ne a yayin da yake yin jawabi a taron kaddamar da ayyuka shida da suka lashe sama da naira miliyan 873.66 a jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da na kwalejin kimiyya da fasaha ta Tatari Ali dukkan su da ke Jihar Bauchi.
- Bauchi Ta Mika Ragamar Filin Jirgin Tafawa Balewa Ga Tarayya
- Gwamnonin PDP Sun Karyata Shirin Mubaya’a Ga Tinubu
Gine-ginen da aka kaddamar sun kunshi tsangayar kimiyya da fasaha da kuma sashen tsangayar fasaha da ke a jami’ar ta Abubakar Tafawa Balewa, sai kuma na dakin taro da dakunan yin gwaje-gwajen magunguna a jami’ar Tatari Ali, wadanda aka gina su daga cikin kudin tallafi na asusun hukumar TETFund na shekarar 2021 zuwa shekarar 2022.
Tinubu wanda ministan kula da harkokin kasashen waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya wakilce shi a gurin taron ya sanar da cewa, bunkasa fannin ilimin zamani na daya daga cikin ayyukan da gwamnatin tarayya a karkashin shugabancin jam’iyyar APC ta bai wa fifiko.
Shugaban ya kara da cewa, kirkiro da shirin bai wa daliban jama’a rancen kudin karatu da gwamnatin ta yi, ta yi don ta saukaka wa daliban wajen gudanar da karatunsu.
Acewarsa, gwamnatin ta kuma gana da kungiyar dalibai ta manyan makaratu ta kasa (NANS) don tattaunawa a kan jin dadi da walwalar dailban.
Ya ce, wannan na daga cikin kokarin da gwamnatin ke kan ci gaba da yi don magance kalubalen da daliban manyan makartun kasar ke fuskatan da kuma samar da kyakyawan yanayi a tsakanin gwamnatin da kuma kungiyon daliban na manyan makaratun kasar nan.
Kazalika, Tinubu ya sanar da cewa, a kwanan baya gwamnatinsa ta dakatar da umarnin ba aikin yi ba biyan albashi da ta kakaba wa kungiyar malaman jami’o’in kasar nan (ASUU), wanda wannan umarnin, ya ba su damar karbar albashinsu da gwamnatin ta rike saboda yajin aikin da suka yi.