Kamfanoni 6 ne suka tafka asarar naira biliyan 166.3 a cikin wata 9, kamar yadda rahoton ayyukansu na karshen watan Satumba na shekarar 2023 ya nuna.
Kamfanonin da suka tafka wannan asarar sun hada da ‘Nestle Nigeria’, ‘Cadbury Nigeria’, ‘Dangote Sugar Refinery’, ‘Nigerian Breweries’, ‘International Breweries’ da kuma kamfanin ‘Champion Breweries’.
- Bauchi Ta Mika Ragamar Filin Jirgin Tafawa Balewa Ga Tarayya
- Gwamnonin PDP Sun Karyata Shirin Mubaya’a Ga Tinubu
Bayani ya nuna cewa, hauhawar kudin ruwa da karyewar darajar naira ne musabbabin asarar da kamfanonin suka tafka.
Karyewar darajar naira ya kai ga kara kudin gudanar da ayyuka da tsadar kayan da ake sarrafa wadanda yawancinsu ana shigowa da su ne daga kasashen waje.
Haka kuma Babban Bankin Nijeriya ya kara kudin ruwa a karo na 8 zuwa kashi 18.75 a ranar 25 ga watan Yuli.
A tsokacinsa, shugaban kungiyar masu masana’anantu na kasa, Francis Meshioye, ya nemi gwamnatin tarayya ta kafa bankin masana’antu wanda za a dora wa alhakin samar wa bangaren masu masana’antu kudaden gudanarwa don samun nasarar ayyukansu.
Meshioye ya kara da cewa, bangaren masana’antun Nijeriya ya gawurtar da ya kamata a samar masa da banki na musamman don kula da yadda ake gudanar da ita musamman ganin bangare na da matukar muhimmanci ga bunkasar tattalin arzikin kasa.
Ya kuma nemi gwamnati ta samar da gidauniya na musamman da masu masana’antu za su rika samun kudaden gudanar da ayyukansu ba tare da ruwa mai yawa ba.