Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Lamido Sanusi, ya shawarci sabon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso, da ya samar dabarun dakile hauhawar farashi a kasar nan.
Tsohon gwamnan babban bankin ya bayar da wannan shawarar ne a yayin da ya jagoranci wata tawagar masana tattalin arziki zuwa babban bankin don tattauna da sabon shugaban bankin, cardoso.
- Ba Mu Janye Tsofaffin Takardun Naira Ba – CBN
- Rashin Tsaro: Za Mu Fara Horar Da Jami’an Sa-Kai Don Tsare Al’ummar Zamfara – Gwamna Lawal
Rahotanni ya nuna yadda hauhawar farashi ke ci gaba da a ‘yan watannin nan inda a halin yanzu ya kai kashi 26.72 a kididdigar da aka yi a watan Satumba 2023.
Sanusi ya nemi hukumar gudanarwa bankin su yi aiki tukuru wajen ganin an rage hauhawar farashin musamman ganin yadda yake shafar harkokin yau da kullum na al’ummar Nijeriya.
Ya kuma nuna muhimmancin shiri mai dogon zango don cimma abubuwan da CBN ya sanya a gaba.
Daga nan ya kuma nemi gwamnati ta bayar da muhimmanci a wajen bunkasa harkar noma, ilimi, musaman ilimin yara mata.
Tunda farko, shugaban CBN, Cardoso ya yi alkawarin cewa, a karkashin jagorancinsa, CBN zai bayar da muhimmanci ne ga tabbatar da farashi da gina tattalin arzikin kasa.