Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa gwamnatinsa na samun ci gaba a yakin da ake yi da ‘yan fashin daji da kuma laifuka a jihar.
Gwamnan jihar Zamfara ya bayyana cewa rukunin farko na kungiyar kare hakkin jama’a (CPG) da aka dauka daga dukkanin kananan hukumomi 14 da za a tura sansanin horo nan da mako guda.
- An Gudanar Da Zanga-zanga A Filato Saboda Soke ‘Yan Majalisar PDP
- Gwamnatin Kano Za Ta Kashe Sama Da Naira Biliyan 40 Wajen Aiwatar Da Manyan Ayyukan Raya Jihar
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce gwamna Lawal ya karbi takardar kwamitin da aka kafa kan tsaro a zauren majalisar da ke gidan gwamnati Gusau.
Ya kara da cewa kwamitin karkashin jagorancin Alhaji Bello Umar Karakkai tsohon shugaban ma’aikata na jihar Zamfara ne ya gabatar da takardar.
“Gwamna Dauda Lawal a lokacin da yake jawabi a lokacin gabatar da takarda kan rahoton kwamitin, ya yaba wa kwamitin bisa kwazon da suka yi na nazarin rahoton da kuma gabatar da matsayin gwamnati kan batutuwa daban-daban da shawarwarin da aka gabatar a cikin rahoton.
“Kwamitin ya sanar da biyan bukatar jama’a wajen nazarin shawarwari daban-daban da kuma batutuwan da kwamitin rikon kwarya na 2023 ya gabatar da kuma fito da matsayin gwamnati. Wannan ya yi daidai da yunkurin gwamnatin Zamfara na magance matsaloli daban-daban da suka shafi aikin gwamnati da na gwamnati baki daya.
“Gwamnan ya kuma yaba wa kwamitin rikon kwarya kan yadda suka yi nazari sosai kan batutuwa da dama da suka shafi ci gaban jihar Zamfara.
“Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta yi amfani da manufofin hadin gwiwa na jama’a wajen gina jihar Zamfara.
“Gwamnatin Jiha ta kuduri aniyar aiwatar da takardar da zarar ta kammala tantance mukamai daban-daban da kwamitin ya dauka.
“Gwamna Lawal ya bayyana kudirinsa na daukar kwararan matakai domin biyan bunkatun da ke kasa. Za mu kafa kwamitocin gudanarwa da na shari’a da na bincike inda bukatar hakan ta taso. Wadannan kwamitocin za su kasance masu muhimmanci wajen bincike tare da magance matsalolin da suka taso.
“Kwamitin gudanarwa zai mayar da hankali kan aiwatar da shawarwari masu amfani da kuma masu alaka da siyasa, yayin da kwamitin shari’a zai binciki batutuwa daban-daban da daidaikun mutane suka aikata tare da aiwatar dokokin da suka dace.”