Babban bankin Nijeriya (CBN) ya sake tabbatar wa ‘yan kasar nan cewar akwai isassun takardun kudi na Naira tare da kwantar da hankalin mutane na daina shiga firgici saboda karancin kudade a bankuna.
CBN, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya sake nanata cewa tsofaffi da sabbin takardun kudi na Naira suna daram.
- An Wayar Da Kan Malamai Game Da Ajiyar Kudin Aikin Hajjin 2024 A Kaduna
- An Kwace Kambun Hilda Baci A Gasar Dafa Abinci Ta Duniya
“Don kaucewa shakku, muna nanata cewa akwai isassun takardun kudi a fadin kasar nan don gudanar da duk harkokin tattalin arziki na yau da kullum,” in ji kakakin CBN, Isa AbdulMumin.
“Saboda haka, an umarci rassan bankin CBN a fadin kasar nan da su ci gaba da fitar da takardun kudi daban-daban na tsofaffi da sabbi cikin adadi mai yawa zuwa bankunan kasuwanci don ci gaba da rarrabawa ga abokan huldar bankuna.
“Muna so mu sake bayyana cewa duk takardun kudi na banki da CBN ke bayarwa suna nan a kan doka. Kamar yadda sashe na 20 (5) na dokar CBN ta shekarar 2007, babu wanda ya isa ya ki karbar Naira a matsayin hanyar biyan kudi.”
CBN “ya sake tabbatar da cewa akwai isassun takardun kudi don saukaka ayyukan tattalin arziki na yau da kullum”.
A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana shirin sake fasalin wasu kudade, sannan ya bukaci ‘yan Nijeriya da su musanya tsofaffin takardunsu kafin ranar 31 ga watan Junairu, 2023.
Wannan hukunci ya haifar da tabarbarewar tattalin arziki yayin da ‘yan Nijeriya da dama suka shiga mawuyacin hali, lamarin da ya haifar da tarzoma a wasu jihohin da kone wasu bankuna da kuma injinan cire kudi.
Daga baya bankin ya amince da tsawaita wa’adin canjin takardun Naira.
Wasu gwamnonin jam’iyyar APC na wancan lokacin sun kai CBN da gwamnatin tarayya zuwa kotun koli inda kotun koli ta yanke hukunci a watan Maris na 2023 cewa tsofaffin takardun kudi na N200, N500, da N1,000 za su ci gaba da aiki har zuwa ranar 31 ga Disamba. , 2023.