Tuni hukumar kwallon kafa ta duniya ta kammala samun kungiyoyin da za su kece raini a gasar ta FIFA Club World Cup da za a gudanar a cikin watan Disambar na wannan shekara.
Ranar Asabar kungiyar kwallon kafa ta Fluminense ta cike gurbin karshe na shida, bayan da ta yi nasara a kan kungiyar Boca Juniors kuma ta lashe gasar Copa Libertadores a Rio de Janeiro, Babban Birnin Kasar Brazil.
Manchester City ce za ta wakilci Nahiyar Turai, wadda za ta fara gasar daga matakin dab da karshe da za a yi gumurzu a kasar Saudi Arabia, kamar yadda hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta tsara.
Ga Yadda Jadawalin wasannin Yake:
Kungiyar Manchester City za ta fafata da ko dai kungiyar Club Leon ko Urawa Red Diamonds ranar 19 ga watan Disamba sai Fluminense za ta kece raini da Al Ahly ko Al-Ittihad ko kuma Auckland City, sannan wadanda suka ci karawar dab da karshe za su hadu a wasan karshe a ranar 22 ga watan Disamba.
Jerin Kungiyoyin da suke cikin FIFA Club World Cup 2023:
Al Ahly (Masar) – Wadda ta lashe kofin zakarun Afirka CAF Champions League 2023.
Al-Ittihad (Saudi Arabia) – Mai masaukin baki, wadda ta lashe gasar Saudi Arabia kakar 2022/23.
Auckland City (New Zealand) – Wadda ta lashe kofin zakarun Oceania a 2023.
Fluminense (Brazil) – Wadda ta dauki Copa Libertadores a 2023.
Leon (Medico) – Wadda ta dauki CONCACAF 2023.
Manchester City (Ingila) – Wadda ta dauki Champions League a 2023.
Urawa Red Diamonds (Japan) – Wadda ta lashe kofin zakarun Asia a 2023.
Wasannin da za a buga a FIFA Club World Cup a Saudi Arabia:
Zagayen farko
Al-Ittihad da Auckland City ranar 12 ga watan Disamba a King Abdullah Sports City, Jeddah
Zagaye na biyu
Leon da Urawa Red Diamonds ranar 15 ga watan Disamba a Prince Abdullah Al Faisal Stadium, Jeddah. Al Ahly da Al-Ittihad ko kuma Auckland City ranar 15 ga watan Disamba a King Abdullah Sports City, Jeddah.
Zagayen karshe
Fluminense da Al Ahly ko kuma Al-Ittihad ko kuma Auckland City ranar 18 ga watan Disamba a King Abdullah Sports City, Jeddah. Manchester City da Leon ko kuma Urawa Red Diamonds ranar 19 ga watan Disamba a King Abdullah Sports City, Jeddah
Wasan neman na uku
Ranar 22 ga watan Disamba a Prince Abdullah Al Faisal Stadium, Jeddah Wasan karshe: Ranar 22 ga watan Disamba a King Abdullah Sports City, Jeddah