Assalamu alaikum, yau ma ga mu a filinmu mai albarka. A wannan makon, mun shigo fannin sutura da shigar da za mu koya wa yaranmu domin an ce da na gaba ake gane zurfin ruwa, haka ne yadda yanayin shigar iyaye take haka yara za su yi. Muddin uwa za ta yi shigar mutunci to yaranta ma za su yi koyi, haka yara maza yanayin shigar iyaye maza yanayin su, muddin da zai zo da dabi’a marar kyau ya na da kyau a take uba ya daure fuska ya nuna masa ba a gidansa ba to in sha Allahu yaro zai ji tsoro ya bar wannan dabi’a da ya samo ta, amma in har za a saka masa ido shi fa ya samu abin da ya ke so domin zai za ta dama abu ne mai kyau, daga haka yara suke zarmewa. Allah Ya ba mu ikon sa ido kan yaranmu.
Ya kasance kullum iyaye idanuwanmu na kan yaranmu sabo da yanayi na rayuwa yanzu da ya canja ba yara ba manya ba mata ba masu aure, duk fa karanci ne na tarbiyya ke jawowa, wasu kuma mu’amala da mutanen wofi ke sawa. zuwa makaranta ya zama dole ga yaranmu daga kan boko har islamiyya ya kasance yara sun horu da wannan tarbiyya kada mu bar yara su dinga yin fashi idan ya saba fashi aiki ya same mu kina ji ki na gani za ki kasa tankwasa shi ya tafi karatun.
Yanzu iyaye ke tsoron yaransu ba yara ke tsoron iyaye ba kawai wai da sunan soyayya wata soyayyar kuma itace sanadin lalacewar yaran, muddin yaro zai yi laifi asa masa ido to wallahi daga baya sai ya zame mana matsala, ya na da kyau a nuna masa yin abu ba daidai ba abu ne mara kyau amma in har zai yi a saka masa ido to fa akwai katuwar matsala a gaba.
- Hana yara
- Yawo gida-gida
- Yawon ball
- Yawon Kududdufi wanka
- Yawon kallo a gidajen kallo.
- Zama cikin unguwa cikin yara marasa aikin yi ko mararsa tafiya makaranta.
- Tafiya biki ko fati
Wadannan na matukar gurbata tarbiyyar yara saboda kowa da abun da zai je ya koyo.
Mu hadu a mako na gaba…