• English
  • Business News
Thursday, October 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

INEC Ta Dakatar Da Zabe A Wasu Sassan Jihar Kogi

by Sadiq
2 years ago
INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da dakatar da gudanar da zabe a wasu wurare a jihar Kogi, sakamakon wasu rahotanni da aka samu na magudin zabe.

An tafka kura-kurai a lokacin zaben, ta hanyar rubuta sakamakon zaben kafin kammala kada kuri’a a kananan hukumomin Adavi, Ajaokuta, Ogori/Magongo, Okehi, da Okene.

  • Allah Ya Yi Wa Fitaccen Tsohon Dan Wasan Hausa, Usman Baba (Samanja) Rasuwa
  • Hanyoyin Tsaftace Jiki Bayan Saduwa

Sai dai lamarin ya fi kamari a yankin Ogori/Magongo.

Hukumar ta yi kakkausar suka ga wadannan abubuwan da suka faru, inda ta bayyana cewa ba za ta amince da lamarin ba.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ya jaddada cewa duk wani sakamakon da bai samo asali ba daga tsarin da hukumar ta kafa a rumfunan zabe ba za ta amince da shi ba.

LABARAI MASU NASABA

An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato

Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson

Wannan lamari ya sanya dakatar da zaben a Unguwa Tara a karamar hukumar Ogori/Magongo—musamman Eni, Okibo, Okesi, Ileteju, Aiyeromi, Ugugu, Obinoyin, Obatgben, da Oturu—a halin yanzu.

Ana ci gaba da gudanar da bincike a wasu kananan hukumomin, kuma za a ci gaba da tattara sakamakon zaben.

A yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, hukumar na bin diddigin ma’aikata da kayan aiki don gano wadanda suka taka rawa wajen tafka magudi a jihar.

INEC ta tabbatar wa masu kada kuri’a a jihar Kogi cewa za a kare kuri’unsu, kuma za a mutunta zabin dimokradiyya.

Hukumar tun a baya ta jadadda kudirinta wajen tabbatar da sahihin zabe.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato
Manyan Labarai

An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato

October 16, 2025
Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson
Manyan Labarai

Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson

October 16, 2025
sallah
Manyan Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ya Ƙara Raguwa Zuwa Kashi 18.02%

October 15, 2025
Next Post
INEC Ta Ayyana Uzodimma Na APC A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Imo

INEC Ta Ayyana Uzodimma Na APC A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Imo

LABARAI MASU NASABA

An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato

An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato

October 16, 2025
Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson

Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson

October 16, 2025
Sashen Cinikayyar Kamfanonin Sarrafa Hajoji Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso 4.7 Bisa Dari Cikin Watanni Tara Na Farkon Shekarar Nan

Sashen Cinikayyar Kamfanonin Sarrafa Hajoji Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso 4.7 Bisa Dari Cikin Watanni Tara Na Farkon Shekarar Nan

October 15, 2025
Kafafen Sada Zumunta Na Zamani Suna Taimakawa Wajen Ta’azzara Matsalar Tsaro A Arewa – Yari 

Kafafen Sada Zumunta Na Zamani Suna Taimakawa Wajen Ta’azzara Matsalar Tsaro A Arewa – Yari 

October 15, 2025
Nazarin CGTN: Jamaar Duniya Sun Yi Ammana Amurka Za Ta Fi Jin Jiki Daga Yakin Haraji 

Nazarin CGTN: Jamaar Duniya Sun Yi Ammana Amurka Za Ta Fi Jin Jiki Daga Yakin Haraji 

October 15, 2025
Kotu Ta Ɗaure Mai Horas Da ‘Yan Wasa Shekaru 8 Sakamakon Zargin Luwaɗi Da Ƙaramin Yaro A Kano

Kotu Ta Ɗaure Mai Horas Da ‘Yan Wasa Shekaru 8 Sakamakon Zargin Luwaɗi Da Ƙaramin Yaro A Kano

October 15, 2025
Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Ƙasar Madagascar

Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Ƙasar Madagascar

October 15, 2025
Shugaban Zaunannen Kwamitin Majalisar Wakilan Jama’ar Sin Ya Gana Da Mukaddashin Shugaban Majalisar Dattawan Kasar Liberia

Shugaban Zaunannen Kwamitin Majalisar Wakilan Jama’ar Sin Ya Gana Da Mukaddashin Shugaban Majalisar Dattawan Kasar Liberia

October 15, 2025
Gwamnan Kaduna Ya Taya Al’Amin Murnar Nasarar Lashe Gasar Ƙirƙirar Fasaha Ta Duniya A Ƙasar Birtaniya 

Gwamnan Kaduna Ya Taya Al’Amin Murnar Nasarar Lashe Gasar Ƙirƙirar Fasaha Ta Duniya A Ƙasar Birtaniya 

October 15, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Ladan Bosso Ya Ajiye Aikin Horar Da Barau Fc 

Da Ɗumi-ɗumi: Ladan Bosso Ya Ajiye Aikin Horar Da Barau Fc 

October 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.