Saboda ya nuna matukar hazaka a kwas din da ya yi sai aka sake bashi dama ya zama cikakken dalibi saboda ya karanta digiri na biyu, ta haka ya samu shaidar takardar digiri na biyu na Harbard MBA a 1959.
Da yaga ya samu damar mallakar gogewa ta aiki da horarwar da ya samu ga kuma ingantaccen karatun da ya yi, sai ya tsaida shawara inda ya auri Miss Abimbola Solomon ranar 1 ga Nuwamba 1959.
- INEC Ta Ayyana Uzodimma Na APC A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Imo
- An Harbe Barawon Akwatin Zabe A Kogi
Basarake Ohinoyi na Ebiraland,Alhaji Ado Ibrahim ya rasu ne da sanyin safiyar Lahadi 29 ga Oktoba 2023.Ya mutu yana da shekara 95 a duniya sanannen dan kasuwa ne wanda ya shahara shi mutum ne mai son ya tafi da yadda zamani ya kasance a rayuwarsa inda ya zauna a birnin Legas ya kwashe shekaru masu yawa.Tsohon Shugaba ne na kamfanin Nestle Nijeriya, an yi jana’izar Ohinoyi na Ebiraland, Dakta Abdulrahman Ado-Ibrahim da karfe biyu na rana.
Sakataren masauratun gargajiya na Ebiraland Alhaji Yunusa Sule shi ya bayyanawa kamfanin dillacin Labarai na Nijeriya kafin a kai ga yi ma shi jana’iza an dauka matakan da za su ta kasance ta girmamawa ce a Okene.Jana’izar an yi ta ne da karfe biyu na rana a Okene bayan an kawo gawarsa daga Abuja kamar yadda Sakataren ya bayyana ya mutu da karfe biyu ne a wni asibitin da ba’a bayyana sunansa ba a Abuja bayan yayi fama da tashin lafiya.Sakataren ya ce mutuwarsa ba karamin rashi aka yi ba a Ebiraland.
Ya ce sun yi rashin“Babansu da kuma Shugaba ranar Lahadi da safe a wani Asibiti a Abuja inda aka gano yana da wata cutar daya dade da fama da ita ta tsufa,rashin lafiya na mako uku.“Mun shiga cikin dimuwa dangane da rasuwarsa lalle uba ne mutumin kirki kuma dalin Shugaba ba wai a sashen Ebiraland ba gaba dayan Kogi da kuma Nijeriya baki daya.Rasuwarsa ta bar wani babban gibin da ba za’a iya cikewa ba.