Tura dai ta fara kai al’umma bango dangane da irin cin kashin da ‘yan bindiga masu garguwa da mutane ke yi, inda wata uwa mai suna Maryam Muhammad ‘yar shekara 52 ta ceci rayuwar danta daga hannun masu garkuwa a kauyen Sabon Garin Jada da ke karamar hukumar Alkaleri a Jihar Bauchi.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, Malama Maryam ta gamu da ajalinta a lokacin da ta kare danta daga hannun masu garkuwa da mutane, inda ta yi kukan kura ta nufi kansu da tabarya har ma ta karya daya daga cikin masu garkuwan, lamarin da ya sanya suka bude mata wuta har ta rasu nan take.
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa, Marigayiya Maryam mai ‘ya’ya takwas a duniya ta nufi kan masu garkuwa da mutanen ne a lokacin da suka mamaye gidanta da ke sabon Garin Jada da nufin su yi garkuwa da danta ko illata shi, inda ta ce sam hakan ba zai yiyu ba.
Idan za ku iya tunawa dai, a ranar Alhamis da ta gabata ne dai wasu gungun ‘yan bindiga suka kashe mutum hudu tare da mutum uku a wani harin da suka kai yankin Alkaleri.
Wakilinmu ya zanta da diyar marigayiyar, Hauwa’u Muhammad ‘yar shekara 26, inda ta yi cikakken bayanin yadda lamari ya faru, ta ce, ‘yan bindigan sun so sace yayanta ne sai kuma mamarsu ta yi kokarin hana su har sai da ‘yan bindigan suka bude mata wuta.
“Da daren ranar Litinin da misalin karfe 12 wasu mutane suka shigo cikin gidanmu tare da kokarin yin garkuwa da yayana. Ita kuma mahaifiyarmu ta taso domin ta taimaka masa, a wannan yanayin ne suka harbe har lahira, inda muke addu’a Allah ya mata rahama,” Hauwau ta shaida cikin kuka.
Ta kara da cewa yayan nata bai mutu ba, amma sun ji masa raunuka a kai. Ta ce ‘yan bindigan da suka shigo gidansu sun kai mutum 11.
Da yake nasa jawabin a wajen jajantawa kan rasuwar marigayiya a ranar Asabar da gabata, gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad Abdulkadir ya ayyana Marigayiya Maryam a matsayin wata jarumar da ta bar abin koyi ga al’umma, ya misalta cewa lokacin da za a ji tsoron ‘yan bindiga ya wuce.
A cewarsa, “Abun da ya faru a wannan garin a gaskiya ya zama abun jaje sosai a garemu. Mun rasa ‘yar uwa, muna fatan Allah ya amshi shahadarta.
Wannan mata ta zama abin koyi a garemu a matsayinta na uwa wacce ta nuna mana mata ma suna iya jajircewa, ba ta yi mutuwar banza ba, ta yi mutuwar shahada insha Allahu, Allah ya jikanta ya rahama.”
Gwamna Bala Muhammad ya daura da cewa, “Mun zo nan garin ne domin mu jajanta muku ga wannan lamari wanda ya zama ruwan dare a Nijeriya.
“A yadda ake ma Jihar Bauchi tana da tsaro, amma abun yana son ya addabemu, sai dai ba za mu kwanta muna barci ba, za mu yi iya bakin kokarinmu mu wajen rayukanku da dukiyarku, kuma ya kamata a sani tsaro abu ne da ya kasance hakki ne a kan kowa.”
Gwamnan ya roki sarakuna da malamai da jama’a da su kara ninka addu’o’i domin samun nasarar shawo kan matsalolin tsaro da suke addabar kasar nan. Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da suke amsa kiran jama’a a kowani tare da hanzarin kawo dauki idan jama’a sun bukaci hakan, musamman a lokacin da suke cikin yanayi na neman agajin gaggawa.
A nasa jawabin, shugaban karamar hukumar Alkaleri, Yusuf Garba ya bayyana cewar suna samun matsalar tsaro a yankinsu ne sakamakon iyaka da suka yi da jihohin Bauchi da Taraba wanda aka kashe mutum hudu a garin, ya nemi hadin kan jama’a domin samun nasara.
Shi kuma kwamishinan ‘yansandan Jihar Bauchi, CP Umar Sanda ya roki jama’a ne da su samar musu da bayanan sirri da zai taimaka wa hukumomin tsaro a kowani lokaci wajen yaki da matsalar tsaro.
A ‘yan kwanakin baya dai an yi ta samu rahotonnin matsalolin tsaro a Jihar Bauchi don ko a kwanakin baya ma an yi garkuwa da Hakimin kauyen Zira da ke karamar hukumar Toro tare da dansa daga bisani aka sako su.