INEC ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Kogi da aka gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba, Ahmed Usman Ododo a matsayin wanda ya lashe zaben.
Ododo ya samu kuri’u 446,237 inda ya kayar da abokin hamayyarsa Murtala Ajaka na jam’iyyar SDP, wanda ya samu kuri’u 259,052, inda dan takarar jam’iyyar PDP, Dino Melaye, ya zo na uku da kuri’u 46,362.
- INEC Ta Bada Umarnin Sake Zabe A Wasu Sassan Jihar Kogi
- Gwamnatin Tarayya Na Hasashen Samun Naira Tiriliyan 45 Daga Harajin Kaya A 2026
Jami’in da ke kula da zaben, Farfesa Johnson Urame ne ya bayyana hakan da misalin karfe 10:25 na daren Lahadi.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, tun da farko dai hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ayyana yunkurin bayyana sakamakon zaben a matsayin wanda bai kammalu ba sakamakon kura-kuran da aka samu a wasu yankunan jihar, musamman karamar hukumar Ogori Magongo, inda aka dakatar da gudanar da zaben.
Biyo bayan dakatar da zaben gwamnan jihar da aka yi a ranar 11 ga watan Nuwamba a wasu sassa a Jihar Kogi sakamakon ganin takardun sakamakon zaben tun kafin a fara kada kuri’a, amma INEC ta ce, za a sake gudanar da sabon zabe a ranar Asabar 18 ga watan Nuwamba, 2023 a rumfunan zaben da matsalar ta faru a unguwanni tara da ke karamar hukumar Ogori Magongo ta jihar.