Kwamishinan ‘yansandan Kano, CP Alhaji Ismaila Shuaibu Dikko da Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero sun haramta hawan dawakin matasa a Jihar Kano baki daya ba tare da samun rubutaccen izini ba daga rundunar ‘yansandan.
Kwamishinan ‘yansanda ya kara da cewa ya ziyarci Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, sun zauna sun tautauna kuma sun amince da haramta hawan dawakin matasa a Kano, domin wanzan da zaman lafiya a jihar.
Ya ce hawan dawakin matasan ba tare da izini ba yana kawo rashin zaman lafiya da karya doka da oda tare da tayar da hankulan al’ummar Jihar Kano.
Haka kuma wakilinmu ya rawaito mana cewa jama’a da dama na kokawa da yadda matasa suke hawan doki tare da janyo asarar rayuka da dokiyoyin al’umma.
Ya kara da cewa hawan dawakin matasan yana janyo sace-sace da ruguza harkokin kasuwanci da raunata mutane da dai sauransu.