Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya yaba wa rundunar sojin Nijeriya bisa ci gaba da samun nasarorin da ake samu a yakin da ake yi da rashin tsaro a fadin kasar.
Ribadu ya yi wannan yabon ne a ranar Litinin a Abuja a taron shekara-shekara na hukumar leken asiri ta rundunar tsaro ta 2023.
- Yanzu-yanzu: Saudiyya Ta Soke Bizar ‘Yan Nijeriya 264 Bayan Sun Isa Jeddah
- Firaministan Pakistan Kakar: Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Tana Girmama Bambance-bambance A Tsakanin Kasa Da Kasa
Ya ce, rundunar sojojin a yanzu sun nuna himma sosai wajen yaki da matsalolin tsaro da suka addabi kasar nan, inda ya ce an samu sauye-sauye masu kyau.
Shugaban bangaren leken asiri ta tsaro (CDI), Maj. Janar Emmanuel Undiandeye, ya ce, rundunarsa a shirye ta ke kan kokarinta na yin amfani da karfin tsarin tsaro don cimma manufofin tsaron kasa.
CDI ya ce, taron na shekara-shekara ana yinsa ne don baiwa hukumar tsaro da leken asiri damar tantancewa da inganta ayyukan sassan tsaronta a kowace shekara.